Me za mu yi kan tsadar abinci?

Daga MARHABA YUSUF ALI

Wai jama’a bai kamata mu dage da maganar tsadar kayan abinci ba kamar yadda muka dage da maganar tsaro kuwa?

Idan kai ka ci ka ƙoshi ba ka tuna wanda tun kafin rayuwar ta yi tsada da ƙyar suke samun abinda za su ci ma balle yanzu da komai ya tashi wani ma ya ninka?

Magidanta da suka ajiye iyali a gida su wuni suna yawo a rana wani da ƙyar zai samu abin da zai ciyar da su sau ɗaya a rana. Wani jarin ma bai kai na dubu biyu ba, me ya samu? Me ya kai gida?

Masu rubutu a kan haihuwa gaba-gaɗi, dama barin mutane ku ka yi suka huta da hayaniyar ku, ku ka yi amfani da damar ku a kan abin da ya dace.

Ku yi ta rubutu a kan gwamnati ta duba lamarin hauhawar kayan masarufi, ku yi amfani da damar ku ta soshiyal midiya ku janyo hankalin gwamnati ta san abun ya damu al’umma.

Wanda matsalar ta fi damu ba su ne a soshiyal midiya ba, kuma ko kai da kake iya siya abun yana ɓata maka rai, ka ga abun da ka siya yau, kana shiga shago ko kasuwa gobe ka ga ya canza kuɗi.

Ban ce laifin gwamnati ne dukka ba, laifin gwamnati na rashin bibiya ne, mutanen da alhakin su ne su yi wannan aikin ba sa yi. Ɗan kasuwa shi zai sa wa kayansa kuɗi yanda ya ga dama. In dala ta hau ko mai ya hau, amma in ta sauka ko mai ba zai canza ba, in kuma ta ƙara hawa kuma haka abun nan zai ƙara hawa bayan da ta sauka bai sauka ba. Masu bada sadaka, masu ɗaukar nauyin NGOs, ku ma ku dage ku ringa yaye wa na kusa da ku.

Wani ga mabuƙata a unguwar sa a maƙota ba zai bayar ba amma sai ya zo yana bayarwa a soshiyal midiya. A ringa nufar Allah da aikin alkhairi don Allah.

Masu wadata mu ringa dagewa in mun yi girki ko mutum ɗaya ka bawa, ko gida ɗaya a maƙota ka ɗan kai ba ka san irin ladan da za ka samu ba. Allah ne kaɗai ya san halin da mutane ke ciki a wannan yanayin. Ba fa gwamnati ce za ta yi mana dukka ba, mu ne za mu dage mu rage wa kan mu raɗaɗin.

A facebook ɗin nan na ga wani post wai a shafin Fauziyya D. Sulaiman wai ‘yan mata na zuwa a ba su Indomie da ƙwai a yi lalata da su. Yadda aka dinga martani abin takaici ne ƙwarai.

Tunda mun gane yunwa na jawo irin wannan lalacewar tarbiyyar bai kamata mu dage wurin ceto Al’umma ba?

Ba sai ɗanka ba, ba sai ɗan wani naka ba, in ka taimaka al’umma ta gyaru kai ma za ka ji daɗin ta, yaran ka za su samu damar rayuwa da walwala a cikin ta.

Ƙananan yara su ringa sace-sace, yaro bai kai ya kawo ba amma ya iya ɗauke-ɗauke, mafi yawa dai ko me ya sata abinci zai siya da kuxin. Shi ɗan adam da abinci yake rayuwa, in dai zai rasa wannan to zai iya shiga kowanne hali. Canjin ya fara daga kan mu, in ka yi abinci ko ‘plate’ ɗaya ne za ka iya bayarwa, ka bai wa mai buƙata.

Yara a unguwa da ka fahimci babu a gidan su ka taimaka musu. Allah ya taimake mu gaba ɗaya, ya ba wa gwamnatin mu ikon gyara kura-kuran ta.

Marhaba matar aure ce `yar asalin jihar Kano, mazauniyar birnin Ikko