Minista ta raba takardun kama aiki da komfutoci 172 ga masu sa ido kan ayyukan inganta rayuwa a Sokoto

Daga UMAR M. GOMBE

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta miƙa takardun kama aiki da ƙananan komfutoci ga ma’aikata 172 waɗanda aka ɗauka domin su sanya ido kan ayyukan inganta rayuwa da ma’aikatar ta ke aiwatarwa a Jihar Sokoto.

A wajen taron raba takardun da komfutocin, ministar ta ce, “Wannan ma’aikata ta ƙaddamar da horas da ma’aikata 5,000 masu zaman kan su da za su sa ido kan ayyukan shirin Haɓaka Rayuwar Al’umma (National Social Investment Programme, NSIP) a Abuja a ranar Alhamis, 4 ga Fabrairu, 2021. An gudanar da horaswar a duk faɗin ƙasar nan, ciki har da Jihar Sokoto, daga watan Fabrairu zuwa Afrilu, 2021.”

A jawabin, wanda wakilin ta a taron, wato Babban Sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alƙali ya karanta, ministar ta ƙara da cewa ta je Sokoto ne domin ta ƙaddamar da raba takardun kama aiki da na’urori ga ma’aikata masu sa ido masu zaman kan su a Jihar Sokoto domin su samu ƙarfin fara aikin nasu.

A sanarwar da mai taimaka wa ministar ta musamman a aikin yaɗa labarai, Halima Oyelade, ta bayar, an ruwaito ministar ta na cewa, “Waɗannan na’urorin an tanadar masu da wata manhaja wadda za a yi amfani da ita a aika da rahoton ayyukan sanya ido da ma’aikatan sa ido masu zaman kan su waɗanda aka horas. Dukkan na’urorin da aka raba domin sa ido kan wannan shiri a nan cikin Nijeriya aka yi su kuma wani kamfani na ƙasar nan ne ya ƙirƙiri ita manhajar da ake amfani da ita wajen aikin sa idon. “

Ministar ta yi kira ga ma’aikatan sa idon masu zaman kan su da kada su kuskura su bada aikin nasu ga wani mutum daban, kuma su yi aiki tuƙuru tare da kishin ƙasa da tsare gaskiya.

Ana sa ran kowane ma’aikacin sa ido ya sanya ido kan wasu keɓaɓɓun masu amfana da Shirin Haɓaka Al’umma (NSIP) a tsawon shekara ɗaya daga watan Yuni 2021 zuwa Mayu 2022.

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda Hajiya Kulu Abdullahi Sifawa ta wakilta, ya faɗa a jawabin sa na maraba cewa jihar ta amfana daga shirin nan na tura tsabar kuɗi (CCT) da shirin ciyar da ‘yan makanta daga gida na ƙasa.

Tambuwal ya yi roƙo ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara kai wa jihar shirye-shiryen agaji, musamman a yankunan karkara inda mota ba ta iya zuwa saboda faɗin jihar.

Daraktan Hukumar Wayar da kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) a jihar, Abubakar D. Mode, shi ma ya yi jawabi inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ba Gwamnatin Tarayya goyon baya domin ta cimma manufofin shirin.

Ya ƙara da cewa manufar shirye-shiryen Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ita ce a kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ya bayyana jin daɗin sa ga ma’aikatar kuma ya yaba wa sashen inganta rayuwa na gwamnatin Jihar Sokoto saboda yadda su ke aiki tare sumul ƙalau da kuma nasarar da su ke samu wajen aiwatar da ayyukan su.

Shi ma jami’in ma’aikatar mai kula da Shirin Haɓaka Rayuwar Al’umma a Jihar Sokoto, Hayatu Tafida, ya yi kira ga ma’aikatan sa ido masu zaman kan su da su saurari masu koyar da su da kyau kuma su bi ƙa’idojin da aka gindaya domin jihar ta ci moriyar shirin sosai.

Ya bayyana Shirin Haɓaka Rayuwar Al’umma da cewa shi ne shirin da ya fi kowane tasiri a kan rayuwar talakawan ƙasar nan.

Wani daga cikin waɗanda aka ɗauka aikin, Yusuf Ibrahim Bassa daga Sokoto ta Arewa, ya gode wa Gwamnatin Tarayya saboda samar da horaswa da kuma na’urorin aiki domin sa ido kan ayyukan shirin na NSIP a jihar.