Gwamnati za ta fara bai wa ma’aikata magidanta hutun jego

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta amince ta soma bai wa ma’aikatanta magidanta hutun jego na kwana 14 a duk lokacin da matansu suka haihu.

Shugabar ma’aikatan gwamnati ta ƙasa, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana haka cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce bai wa ma’aikatan hutun jegon daidai yake da tanade-tanaden Kundin Dokokin Ma’aikatan Gwamnati na 2021.

Gwamnati ta ce hutun na kwanakin aiki 14 ne amma ban da ranakun Asabar da Lahadi, kuma sau ɗaya a cikin shekara biyu.

Yemi-Esan ta ce, sanarwar hakan ta fara aiki ne daga ranar 25 ga Nuwamban 2022.