Daga NASIR USMAN KAROFI a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za ta saurari koke-koken jama’a kan sabon ƙudirin haraji da ta miƙa gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Idris ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yau, inda ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya umurci ma’aikatar shari’a da ta yi aiki tare da Majalisar Tarayya kan ƙudirin gyaran harajin.
Bugu da ƙari ministan ya ba da tabbacin cewa za a warware matsalolin da ake da su a ƙudirin, kuma babu ƙamshin gaskiya kan zargin cewa za a ƙara wa talakan Nijeriya sabon nauyin haraji ko kuma a durƙusar da wasu cibiyoyi ko hukumomi da ke aiyukan raya ‘yan ƙasa irinsu NASENI, NITDA da sauransu.
Ministan ya gargaɗi ‘yan ƙasa da su guji yaɗa labaran ƙarya, domin suna da illa da raba kan al’ummar ƙasa.