Gwamnatin Bangladesh ta hana layya da saniya mai kama da Trump

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata zabiyar saniya da aka haifa a ƙasar Bangladesh, wadda ta shahara a kafafen sada zumunta saboda kamanninta da shugaban Amurka Donald Trump, ta tsallake rijiya da baya daga yankar Layya bayan gwamnati ta bayar da umarnin a kare dabbar saboda irin ƙimarta ta musamman.

An fi sanin dabbar da laƙabin “Trump” ne saboda irin gashin kanta mai launin zinariya da ke kama da salon gashin shugaban Amurkan.

Tun farko dai an shirya yankar saniyar ne a lokacin bikin Babbar Sallah da aka gudanar ranar Alhamis a Bangladesh, inda miliyoyin dabbobi ke shiga cikin hadayar Layya a kowace shekara.

Sai dai dabbar mai nauyin kilo 700 ta ja hankalin jama’a sosai bayan hotunanta da bidiyonta sun bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya sa mutane da dama suka riƙa tururuwar zuwa domin ganin ta da ɗaukar hotuna.

Mai kula da Gidan Ajiye Dabbobi na ƙasa a Bangladesh, Atiƙur Rahman, ya tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen karɓar dabbar domin kula da ita.

Ya ce, an tanadi keɓaɓɓen rumfa domin saniyar tare da ware mai kula da ita, yana mai ƙarawa da cewa za a killace dabbar na tsawon makonni biyu bayan isa gidan namun daji domin tabbatar da lafiyarta.

Mamallakin dabbar, wani manomi mai suna Zia Uddin Mridha mai shekaru 38, ya bayyana cewa mutane ne suka fara kiranta “Trump” saboda irin gashinta na musamman.

A cewarsa, tun bayan da dabbar ta fara shahara, iyalai da masu sha’awar ganin abubuwan ban mamaki suna yawan zuwa gonarsa domin kallonta kafin daga bisani ya sayar da ita gabanin bikin Layya.

Sai dai hukumomi suka shiga lamarin bayan Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta ƙasar ta nemi a hana yankar dabbar saboda kasancewarta irinta ba kasafai ake samu ba.

Jami’in rundunar ‘yan sanda na yankin Keraniganj da ke birnin Dhaka, Mohammad Ruhul ƙuddus, ya ce sashen kula da dabbobi ne ya nemi taimakon ‘yan sanda domin tabbatar da an kwashe dabbar daga hannun mai ita cikin tsaro.

Ya ƙara da cewa hukumomi sun yi la’akari da cewa dabbar har yanzu tana da ƙuruciya kuma za a iya kula da ita na dogon lokaci domin ta kasance abin tarihi da jan hankali.

Ana sa ran sama da dabbobi miliyan 12 da suka haɗa da shanu, awaki, tumaki da baƙaƙen shanu za a yanka a bikin Eid-el-Adha na bana a Bangladesh.

By ukarofi