Gwamnatin Borno za ta rufe makarantu 300 masu zaman kansu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Fiye da makarantu masu zaman kansu 300 a Borno su na fuskantar barazanar rufewa saboda gaza shiga cikin takardar izinin gwamnati.

Kwamishinan Ilimi Injiniya Lawan Wakilbe, ya shaida wa manema labarai a Maiduguri a ranar Laraba cewa, matakin ya zama dole domin daƙile yaduwar ayyukan wasu makarantu masu zaman kansu.

Ya ce akwai damuwa cewa tun da aka fara atisayen a shekarar 2022 makarantu masu zaman kansu 266 ne kawai suka cika sharuɗɗan, daga cikin kusan 600.

Wakilbe ya ce ma’aikatar, masu makarantu masu zaman kansu, ma’aikatar shari’a da ’yan sanda za su yi taro a ranar Asabar don yin gargaɗi kan haramcin gudanar da makarantun da ba a amince da su ba.

Ya kuma ƙara da cewa, taron zai kuma yi gargaɗi game da yiwuwar rufe makarantun da suka gaza da kuma gurfanar da masu mallakarsu.

“Muna iya sake buɗe filin rajistar na wani dan gajeren lokaci don cikawa na ƙarshe kuma hakan zai faruwa ne ko da bayan an samu amincewar majalisar zartarwa ta jiha,” inji kwamishinan.

Wakilbe ya kuma shaida wa manema labarai cewa, Borno na sanya kima sosai a fannin ilmin fasaha da na sana’o’i ta yadda za a samar da waɗanda suka kammala karatunsu waɗanda za su iya dogaro da kansu.

“Daga cikin yara miliyan 1.8 da ba sa zuwa makaranta, akwai adadi mai yawa sun zarce yawan lokutan makaranta.

“Yaron da yake ɗan shekara huɗu a lokacin da aka fara rikicin Boko Haram a yanzu yana kusan shekara 15 kuma wanda ya kai shekara 10 a lokacin yana da shekara 20 a duniya. Yawancinsu sun girma ne a sansanonin ’yan gudun hijirar.

“Hanya mafi kyawu don kula da irin waɗannan yaran ita ce ta hanyar ilimin boko, ƙididdigewa da ƙwarewar fasaha ta yadda za su iya ɗaukar rayuwarsu,” in ji Mista Wakilbe.

Ya ƙara da cewa, makarantun fasaha da na sana’o’in hannu sun shahara sosai, wanda a lokacin da gwamnati ta je raba fam 450 a sabuwar cibiyar koyar da sana’o’i da aka kafa a karamar hukumar Biu, kimanin mutane 5,000 ne suka fito.

Wakilbe ya ce dole ne Gwamna Babagana Zulum ya amince da zama na safe da na rana ga makarantar da sauran matakan da za su ba ta damar ɗaukar nauyin ɗaliban da suke so.

“Labari daya ne a ƙaramar hukumar Shani. Muna daf da ƙaddamar da ƙarin makarantun fasaha da na sana’a a ƙananan hukumomin Magumeri da Mafa,” in ji Wakilbe.