PDP ta zargi gwamnatin Kebbi da almubazzarancin Biliyan N20 cikin kwana 100

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Jam’iyyar PDP ta adawa a Jihar Kebbi ta zargi gwamnatin jihar ta Kebbi da almubazzaranci da zunzurutun kuɗi har Naira billiyan ashirin a cikin kwanaki 100 kacal.

Alhaji Usman Bello Suru shugaban jam’iyyar PDP ne ya bayyana haka a wata zantawa da manema labarai a garin Birnin Kebbi, yayin da gwamnatin ke gudanar da bikin cika kwanaki 100 da gwamnatin APC ta yi a kan mulki.

Ya ce ta yaya gwamanti za ta kashe har Naira billiyan 20 wajen gyaran babban birnin jihar kaɗai ba tare da la’akari da irin yadda yanayin al’umma ya ke ba. “

Yankin ƙasar Zuru yana fama da rashin hanya na tsawon lokaci wanda ya yi sanadiyyar kariyar tattalin arzikin ‘yan kasuwa da dama musamman masu harkar kayan amfanin gona da Naira billiyan bakwai za ta iya magance wannan matsalar.

“Kawo yanzu gwamnan ya kashe kimanin Naira billiyan 2 a tafiye-tafiye ciki da wajen ƙasar nan a cikin waɗannan ‘yan kwanakin alhali akwai sama da mutum dubu goma da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka ɗaiɗaita suka raba su da gidajensu da gonakinsu,” inji shi.

Suru ya zargi gwamnatin da wawashe dukiyar jiha da sunan ƙawata gari guda kaɗai tare da raba kwangiloli don kawai a azurta waɗansu ‘yan tsirarrun mutane musamman a wajen kwangilar iyar da sakateriya da aka ware har naira billiyan goma wanda a maimakon haka ya kamata ya mayar da hankali wajen nemo hanyoyin warware matsalar tsaro da talauci da yunwa da suka addabi al’umma.

Ahmed Idris shi ne babban Sakataren yaɗa yada labarai na gwama Malam Nasir Idris ya bayyana cewa wannan magana ce ta adawa saboda ganin irin cigaban da gwamnatin ta kawo a cikin kwanaki dari, yana da damar fadar albarkacin bakinsa saboda ba a hana kowa ya fadi ra’ayinsa, amma maganar gaskiya al’ummar jihar Kebbi bisa ga ganin kamun ludayinsa har ma da wadansu daga cikin wadansu masu adawa sun soma yabon wannan gwamanti.

Ahmed Idris ya nemi masu cigaba adawa da su mayar da wuƙarsu cikin kube su zo a haɗa hannu kowa ya bayar da ta sa gudummawa don a ciyar da wannan jiha gaba.