Gwamnatin Jihar Ribas ta buƙaci NBA ta dawo mata da Naira Miliyan 300

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnatin Jihar Ribas ta buƙaci ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) da ta mayar da kuɗi Naira miliyan 300 da aka biya domin karɓar baƙuncin babban taron ƙungiyar na shekarar 2025 da aka ɗage daga Fatakwal zuwa Enugu. Gwamnatin ta bayyana rashin jin daɗin ta kan yadda NBA ta gaza mayar da kuɗaɗen duk da cewa ta sauya wurin gudanar da taron.

A wata sanarwa da mai taimakawa kamtoman jihar kan harkokin yaɗa labarai, Hector Igbikiowubo ya fitar, gwamnati ta ce NBA ta nuna rashin adalci da rashin mutuntawa bayan ta zargi gwamnatin jihar da take demokiraɗiyya. Sanarwar ta ce ƙungiyar ya kamata ta tsaya kan gaskiya da daidaito ta hanyar mayar da kuɗaɗen da ta karɓa.

Gwamnatin ta ce naɗin Kantoma na jihar ya samu ne bisa tsarin doka, tare da jaddada cewa kotun ƙoli ta tabbatar da ingancin matakan da aka ɗauka a jihar domin dawo da zaman lafiya da tsarin dimokuraɗiyya.

Gwamnatin ta buƙaci NBA da ta daina yaɗa kalaman da za su haddasa fitina, tare da buƙatar haɗin kai domin ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi