
Daga BELLO A. BABAJI
An sake samun wani farmaki daga wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a ƙauyen Bayibiki na Ƙaramar Hukumar Tsafe dake Jihar Zamfara, inda aka ƙone masallacin Juma’a da wani ƙaramin Asibitin gwamnati (PHC) gami da gidaje 10.
An yi zargin cewa ƴan bindigar, waɗanda makusantanta ne ga shahararren jagoransu, Adamu Aliero ne suka kai harin a matsayin ramuwa ga kisan ƙanin Aliero, Isuhu Yellow da ɗansa a wani farmakin jami’an tsaro makonni uku da suka gabata.
Lamarin ya auku ne a ranar Asabar da misali ƙarfe 8 na dare, inda bayan haka ne maharan suka fice ba tare da kisa ko garkuwa da kowa ba.
Haka kuma shaidu sun bayyana cewa, maharan sun kai hari a ƙauyen Tsageru a safiyar ranar tare da ƙone wasu gidaje.
Wani shaida ya ce, tun daga mutuwar Isuhu Yellow ne suka shiga halin barazana na harin ƴan bindigar a yankunansu.
Lamarin ya nuna yadda ƙauyuka a jihar ke cigaba da fuskantar barazanar tsaro duk ƙoƙarin gwamnatocin tarayya da jiha na daƙile ayyukan ta’addanci a jihar da ma Shiyyar Arewa maso Yammacin Nijeriya baki ɗaya.
