Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Kaduna ta ɗauki sabbin ma’aikatan lafiya 1,800 domin inganta harkokin lafiya a jihar.
Farfesa Bello Yusuf-Jamo, babban sakataren a hukumar lafiya ta jihar, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi na raba takardar aiki ga sabbin ma’aikatan a ranar Litinin a Kaduna.
Ya ce, an raba takardun ɗaukar aikin na zuwa ne bayan kammala jarrabawar ta baki da rubutu da aka yi a yayin tantancewar domin tabbatar da an yi komai a buɗe da cancanta.
Yusuf-Jamo ya ce, jarin sunayen waɗanda aka ɗauka aikin an kafe su ne a shalkwatar hukumar domin bai wa waɗanda suka samu gurbin aikin gane ko sun samu nasara da karɓar takardun shaidar ɗaukar su aiki.
Sakataren ya ce, ɗaukar ma’aikatan na zuwa ne bayan umarnin da gwamna Uba San ya bayar da amincewa a ɗauki ma’aikata 1,800 a cikin wa’adin mulkinsa biyu a matsayin wani ɓangare na kawo sauyi a fannin lafiya a kiwon lafiya a matakin farko da cike giɓin ma’aikata da ake fama da ita.
Wannan shiri ya ce, ya zaɓa wani babban ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin na farfaɗo da kayayyakin more rayuwa na sama da kaso 70% a asibitoci a matakin farko guda 1,119 da suke faɗin jihar.
Yusuf-Jamo ya ce, tantancewar an yi ta ne bisa adalci domin tabbatar da cewa duk wanda ya cancanta ya samu damar.
“Hukumar ta yi bi matakai masu tsauri na yin komai a buɗe da nuna ƙwarewa a yayin ɗaukar ma’aikatan domin tabbatar da sahihancin tsarin.”
“A rarraba gurbin ɗaukar aikin daidaiwadaida a tsakanin ƙananan hukumomin jihar 23,” ya faɗa.
Yusuf-Jamoh ya ce, ana shirin ɗaukar ƙarin wasu ma’aikatan 1,800 kashi na biyu na ma’aikatan.
Ya kuma ce za a ci gaba da ɗaukar ma’aikata na shekara-shekara domin magance ƙarancin ma’aikata a asibitoci a matakin farko.
A yayin taya sabbin ma’aikatan samun gurbin aikin, Yusuf-Jamo ya buƙace su kasance masu mayar da hankali da nuna hazaƙa da kula da aikinsu yadda ya kamata.
