Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da ranar fara hutun babbar sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kai na ma’aikatar, Misbahu Yakasai, ya fitar ranar Laraba, an bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana za su fara hutu daga ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, 2026, sannan su koma makaranta ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, 2026.
Sanarwar ta kuma ce makarantun je ka dawo za su tafi hutun sallah daga ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2026, tare da komawa karatu ranar Litinin, 1 ga watan Yuni, 2026.
Kazalika, ma’aikatar ta buƙaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar sun je sun ɗauki ’ya’yansu a ranar rufe makarantu tare da mayar da su a ranar da aka tsara domin komawa makaranta.
A nasa saƙon, kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dakta Ali Makoda, ya taya ɗalibai, malamai, iyaye da ɗaukacin al’ummar ɓangaren ilimi murnar babbar sallah, tare da yi musu fatan gudanar da bukukuwan cikin zaman lafiya da annashuwa.
