Gwamnatin Kano ta bai wa makarantun firamare da sakandare hutun Ramadan

Daga WAKILINMU

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta amince makarantun firamare da sakandare a faɗin jihar su tafi hutun ƙarshen zango na biyu da watan Ramadan daga ranar Alhamis, 7 ga Afrilun 2023.

Gwamnatin jihar ta yi kira ga iyayen ɗaliban da ke makarantun kwana jihar da su je su kwashi ‘ya’yansu ranar Juma’a da safe.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ma’aikatar ta fitar ta bakin Daraktan Wayar da Kan Jama’a na ma’aikatar, Aliyu Yusuf.

Yusuf ya ce ana sa ran ɗaliban da ke makarantun kwana su dawo hutu ya zuwa ranar 30 ga Afrilun 2023, yayin da ‘yan je-ka-ka-dawo za su koma ran 1 ga Mayu, 2023.

Ma’aikatar ta yi kira ga iyayen ɗalibai da su kula da ranakun komawa makaranta da aka tsayar don bai wa ɗalibai damar komawa makaranta a kan lokaci.

Ta yi gargaɗin za a ɗauki matakin ladabtarwa kan duk ɗalibin da ya saɓa lokacin komawa makaranta.

Kazalika, ma’aikatar ta yi wa iyaye da ɗalibai fatan a sha hutu lafiya da fatan a yi Ramadan cikin ƙoshin lafiya.