Marubucin gaske ba ya rubutun batsa – Lawan PRP

“Marubuta na da rawar takawa a gwamnati”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubuta mutane ne masu hazaƙa, musamman a ɓangaren fasaha da hikima ta hanyar qirqirar abubuwa na faɗakarwa da isar da saqonni, daga cikin su akwai waɗanda ake iya kira da ýan baiwa, saboda irin basirar da Allah Ya ba su. Malam Muhammad Lawan PRP ɗaya ne daga cikin irin waɗannan marubuta masu baiwa iri daban daban. Bayan kasancewarsa marubucin labaran zube, har wa yau yana rubutun labaran wasan kwaikwayo, da rubutattun waƙoƙin Hausa, kuma ya shahara sosai a wannan ɓangaren, duk kuwa da kasancewar bai fitar wani littafi da ya shahara a kasuwar adabi ba, amma ya rubuta finafinai da suka yi fice a wajen masu kallo. Marubuta da dama na girmama irin sadaukarwar sa, hazaƙarsa da himmar da yake da ita a harkar rubuce rubuce. Wakilin Blueprint Manhaja ya zanta da wannan fasihin marubuci, wanda ya bayyana masa irin nasarorin da ya samu da suka haɗa da kyaututtuka da lambobin yabo da dama.

MANHAJA: Ko za ka fara da gabatar mana da kanka?

MALAM LAWAN PRP: Assalamu alaikum warahmatullahi Ta’ala wabarakatuhu. Sunana Lawan Muhammad PRP kuma marubucin litattafai ne ni da waƙoƙi da kuma fina-finai.

Menene taƙaitaccen tarihin rayuwarka?


An haife ni a garin Kano Ƙaramar Hukumar Tarauni a lokacin tana ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Nasarawa. Haka kuma na yi karatun firamare a Ƙaura Goje Primary School dake Unguwar Gama C. a mazaɓar Kaura Goje Ƙaramar Hukumar Nassarawan Jihar Kano, daga nan sai na tafi makarantar sakandire ta GSS Stadium inda na kammala a shekarar 1997 daga nan ban samu damar ci gaba da karatu ba sai a shekarar 2009 zuwa 2010 inda na maimaita karatu a CAS Kano, sai kuma yanzu da nake shirye-shiryen ci gaba da karatu in sha Allahu.

Yaya aka yi ka samu laƙabin PRP?

(Dariya) PRP sunan unguwarmu ne, tana nan cikin Brigade a Gama C, yadda kowa yake alfahari da sunan unguwa ko garinsa haka nake alfahari da unguwar PRP.

Ba mu labarin gwagwarmayar da ka sha ta karatu da ƙoƙarin da ka yi har rayuwar ka ta zama yadda ka ke a yau.
Na taso a rayuwata ne iyayena ba masu ƙarfi ba ne sosai, hakan ya sa na dinga samun matsaloli a wajen karatuna ina yi ina tsayawa har Allah Ya kawo ni wannan lokacin.

Batun samun matsayi ko daraja wannan abu ne daga Allah, amma zan iya cewa rubutu da karatu su suka zama jigo a rayuwata. Na kasance mayen karatun littafi ne ni, musamman na Hausa, sannan ma’abocin son jin labari ne, ina tsammanin wannan ne ya sa na ji ni ma ina sha’awar rubuta littafi nawa na kaina.

Gwagwarmaya kam an sha ta sai dai lokaci ba zai bari na kawo abubuwan duka ba, na san dai na fara rubutu tun ina firamare aji huɗu inda nake kwaikwayon wani labari na ‘yan gwaigwai mai suna ‘Ɗan Ɓuruntu’, da ake bugawa a wata mujalla da aka yi yayinta a shekarun baya ana kiranta ‘Abin Dariya’.

Labarin yana tafiya ne da hotuna sai na dinga kwatanta yadda ake yi ina samar da labarai, har zuwa lokacin da na fara ganin littattafai na kuma fara bibiyar su ko na ara ko na saya da kuɗina wannan ya faru ne a lokacin da nake karatun sakandire, har Allah Ya haɗa ni da gogaggun marubuta suka ƙara ɗora ni a hanya tare da ba ni ƙwarin gwiwa, har Allah Ya sa aka kawo yanzu.

Menene ya ja hankalinka a harkar rubuce rubuce?

Babban abinda ya ja hankalina ga rubuce-rubuce shi ne, isar da saƙo da kuma bunƙasa adabi. Akwai abubuwa da yawa da na fahimci idan ba ta hanyar rubutu ba ba yadda za a yi a saurare ka. Zan iya cewa rubutu hanya ce ta isar da sako shi ne abin da ya ja hankalina.

Wanene farkon madubinka, wanda ya fara yi maka jagora farkon fara rubutunka?

Wanda ya ja hankalina ya kuma zame mini madubi a yayin rubutuna shi ne Bala Anas Babinlata, tun daga lokacin da na karanta littafinsa ‘Kulu’ sai abin ya birge ni har na fara tunanin ni ma zan iya rubuta labari makamancinsa, sai dai a lokacin da na shiga cikin marubuta akwai waɗanda suka zame mini kamar iyayen gida, irin su Muhammad Lawal Barista, Abdulkarim Papalaje, Ibrahim Birniwa da sauransu. Waɗannan mutane sun taka rawa muhimmiya a fagen samun bitata ko kuma horo a fannin rubutu. Haka kuma har yanzu suna ja mini gora.

Wanne littafi ka fara rubutawa, kuma ya ya ka samu buga littafinka na farko?

Littafina na farko sunansa ‘Zainabu Abu’, amma har yanzu bai shiga kasuwa ba duk da akwai gajerun labarai da nake rubutawa don karantawa a wurin tarurrukan marubuta. Har yanzu littafina na farko da zan ce zai fito a matsayin littafi bai shiga kasuwa ba, ana aikinsa ne, shi ne littafin ‘Zinatu’. Ina fata ya zama na farko.

Na rubuta litattafai da yawa da suka haɗa da; ‘Zainabu Abu’, ‘Baqin Dare’, ‘Kwanan Gida’, ‘Gidan Haya’, ‘Ɓadda Bami, ‘Ragas’, ‘Dokin Zuciya’, ‘Zinatu’ da sauransu. Sai dai kamar yadda na faɗa da farko ba su shiga kasuwa ba har yanzu suna ajiye.

Wanne irin salon labari ka fi rubutawa? Ba mu labarin wasu daga ciki?

Akasarin labaran da nake rubutawa sun ƙunshi rigingimu ne ko laifuka, wato crime story. Kamar ‘Zainabu Abu’ labarin wata mata ce Zainab da ta kashe wani saurayi da take mutuwar so bisa kuskure, ga ta kuma matar aure.

Sai labarin ‘Kwanan Gida’ shi kuma ya ƙunshi labarin wata yarinya Rabi’at da ƙawarta Nusaiba ta ɗora ta a hanyar kwanan gida inda ta haɗa ta da masu kuɗi ‘yan bariki, inda ta kwana uku a gidan wani Alhaji Sani a ƙarshe ta gano ashe mai sana’ar saye da sayar da sassan jikin mace ne. A ƙarshe dai Rabi’at ta shiga bala’in da ya janyo mata yin nadamar shiga bariki.

Sai kuma labarin ‘Ɓadda Bami’ wanda ake kashe wani mutum da budurwarsa a ƙone su a mota tare, a garin binciken ‘yan sanda suka gano kisan yana da alaƙa da rigimar wani kamfani da ake yi kasancewar shi magidancin (Nura) shi ne sabon Manajan da aka naɗa, kafin shi kuma an kashe manajoji da yawa. Kusan dukkan labaraina sun ƙunshi laifuka ne da bincike, ina son irin waɗannan labaran.

Wanne abu ne ya faru da kai a matsayinka na marubuci wanda ba za ka tava mantawa da shi ba?

Akwai wani lokaci da na yi wasu rubuce-rubuce a soshiyal midiya a wani tsohon shafina na facebook, littattafai ne na rubuta na kuma taskace su amma aka samu wani ya lalata mini shafin bisa zargi maras tushe. Na yi matuƙar takaici, duk da dai labaran suna kaina amma yadda na daɗe ina rubuta su zai yi wahala na sake samun wannan damar, domin na rubuta su ne kafin na yi aure, a yanzu kuwa ɗawainiya ta yi yawa ga iyali ga kuma iyaye don haka ina fama da ƙarancin lokaci, ga shi an ce ba a ɓari a kwashe daidai. Wannan abin ya kashe ɓarin zuciyata. Sai dai Alhamdulillahi an samu nasarori daga baya, su ma abubuwa ne da ba zan tava mantawa da su ba.

Shin kana da wata dangantaka ne da aikin jarida?

Ina da dangantaka ƙwarai da aikin jarida, tun da ina rubutu, duk marubuci kuwa tamkar ɗan jarida yake ko in ce Danjuma ne da Danjummai. Kuma ina aiki da Mujallar Fim da ake bugawa duk wata a matsayin mai sharhin littattafai. Marubuci kuma babban ɗan jarida Malam Ibrahim Sheme shi ne jagorana a wannan ɓangaren.

Ko za ka bayyana mana yadda ka samu kanka a matsayin marubucin finafinai?

E, da ma tun shigowata harkar rubutun zube ina sha’awar yadda ake rubutun fim, to kuma sai ya zama ita kanta masana’antar finafinan Hausa (Kannywood) na buƙatar marubuta, matasan marubuta irin su Nazir Adam Salih, Ibrahim Birniwa, Abdulkarim Papalaje, Fauziyya D. Sulaiman, Iliyasu Umar Maikudi da sauransu sai suka fara shirya mana bitoci a tarurrukan marubuta daban-dabam don ƙyanƙyasar sabbin marubuta labaran fim.

Na samu kaina a cikin waɗanda suka shiga sahun bitar har na samu abin da ake so a samu. To, a hankali kuma sai aka fara samun ayyukan rubutun ta hannun dai waɗannan mutanen har zuwa lokacin da aka kawo yanzu da zan iya cewa ni marubucin finafinai ne.

Yaya alaƙar marubuta da masu finafinai, ana sayen labari da daraja kuwa ko ana samun ƙalubale?

A harkar rubutun labarin fim babbar matsalar da ake fuskanta da farko ita ce, ka samu ma a karve ka a matsayin marubuci. Domin duk ƙwarewarka tambayar farko, wanne fim ka tava rubutawa? Harka ce wadda ba ta yiwuwa sai da jagora ko da kana da ƙwarewa.

Ana samun matsala wajen biyan hakki ƙwarai ita ce matsala ta biyu, ko kuma a dinga biyan mutum da kaɗan ta yadda ba zai mori kuɗin ba, duk da akwai masu biyan hakki ma fiye da yadda aka zata, wancananka su suka san darajar rubutu, sannan wani lokacin ana samun canza labari in aka ga ba za a iya abin da ka rubuta ba. Gaskiya akwai ƙalubale masu yawa, saboda masana’antar Kannywood daban ce.

Finafinai nawa ka ke da hannu wajen rubuta su?

Suna da yawa gaskiya, duk da cewa yanzu ana yayin rubuta masu dogin zango ne (series film) waɗansu ni na rubuta su ni kaɗai yayin da wasu kuma hannuwa da yawa ne ciki har da ni muka yi haɗaka.

A cikin waɗanda muka yi haɗaka wajen rubuta su akwai; ‘Gidan Dambe’ na kamfanin Rarara, ‘Sirrin Ɓoye’ na kamfanin Sirrinsu Media, ‘Kan Ta Kile’ na abokina matashin marubuci Zubairu M. Balannaji da sauransu. Sai kuma waɗanda na rubuta akwai; ‘Nasara’, ‘Kwaɗayi’, ‘Mazari’, ‘Tarko’ da sauransu, sai kuma waɗanda nake kan rubutawa yanzu za su kai guda biyar.

Na ji cewa ban da rubutun zube da na wasan kwaikwayo har waƙoƙi ma kana rubutawa.

E, na kan rubuta waƙoƙi, sai dai ba waƙoƙin finafinai ba ne, rubutattun waƙoƙin Hausa ne da kuma ƙasidun yabon Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Duk da ban mayar da hankali kan waƙa sosai ba amma na taɓa lashe gwarzon rubutacciyar waƙa da aka saka gasa akan matsalar fyaɗe a Qasar Hausa. Wannan ita zan kira nasara ta farko a rubutacciyar waqa, sai dai ina nan kan rubuta wasu, domin ina da burin rubuta kundin waƙoƙi kamar yadda Diwanin Ala yake ko kuma Fasaha Akiliyya na Akilu Aliyu.

Yaya ka ke ganin sauyin da aka samu a harkar rubutun adabi, daga wallafar littafi zuwa yanar gizo, wanne cigaba ko ƙalubale hakan ya kawo?

Kamar yadda ka fada, tabbas an samu ƙalubale da kuma cigaba, bari in fara da ƙalubalen. Na farko hakan ya rage yawaitar bugaggun littattafai a hannun mutane, abin da ya janyo kashe sana’ar wasu kamar ‘yan kasuwa da ma’aikatan ɗab’i, sannan ya ƙarfafa sana’ar satar fasaha kai tsaye, ta yadda ɓarawon ba zai ɓata lokaci ba kawai zai yi copy and paste ne ya tura a duk shafin da yake so, sannan ya sanya kuɗi a dinga biyansa yana ci da gumin wani, sannan hukumar da aka bai wa aikin tace littattafai ko ɗab’i ba za ta yi aiki yadda ya kamata ba, domin kowanne kare da doki zai iya rubuta abin da yake so ba tare da sun tace ba, zai iya saki a soshiyal midiya. Abu mafi muni ma shi ne yadda ya haifar da marubutan batsa suke baza kolinsu ba tsoro. Kaɗan daga ciki ke nan.

Duk da akwai tsari na samar da littattafai kai tsaye a manhajar Okada Books da sauran manhajoji na tallata littattafai a yanar gizo, sannan kuma hakan ya kawo cigaban samuwar littattafai a yanar gizo wanda yake sauƙaƙa wa makaranta wajen bincike ta yadda ko babu littafi a kasuwa za ka iya hawa ka sauke ka karanta abinka ko ka karanta ka bar shi.

Akwai kuma tafiya da zamani wanda hakan zai kawo sabon samfurin kasuwancin littafi a sama, ka ga an kawo ƙarshen matsalar ha’incin wasu ‘yan kasuwa wajen tallata ko sayar da littafi ba bisa ƙa’ida ba. Sai kuma matuƙar amfani wajen taskace littafi, wanda har yanzu litattafanmu na Hausa ba su da wannan tagomashin, sau nawa za ka ji marubuci na cigiyar wani tsohon littafinsa?

Wanne abu ne yake hana tsofaffin marubuta irin ka yin rubutu ta yanar gizo?

Satar fasaha, da kuma ci da gumin marubuci. Na sha sakin labarai sai wani ya kwafa ya yi fitar a matsayin nasa. Amma zan fara idan na gamsu da sabon tsarin da ake son kawowa wanda zai ba da kariya da tsaro ga haƙƙin mallakar marubuci.

Wacce gudunmawa tsofaffin marubuta irin ka za ku bayar don tallafa wa masu tasowa?

Gudunmawar da za a iya bayarwa ba za ta wuce ta shawarwari da sanar da su abin da Allah Ya sanar da mu ba. Duk da dai cewa ni ma ban wuce a ba ni shawara ba kasancewata ƙarami a marubutan. Na farko shi ne samar da horo akan rubutu, domin yadda yanayin rubutunmu na Hausa yake a yanzu akwai buƙatar gyara sosai.

Ɓullowar soshiyal midiya ta sa kowa na ɗaukan alƙalami yana yin gaban kansa, su daina damuwa da ɗaukaka (domin ta Allah ce) sannan idan suka yi rubutu kada su saki har sai sun bayar an duba musu, sannan su nemi ilimi a kan rubutu. Ƙofa a buɗe take ga duk mai neman gudunmawa a kan rubutu, akwai irina da yawa da a shirye suke su taimaka wa masu sha’awar rubutu.

Ƙaruwar marubutan batsa a harkar rubutun adabi, na kawo barazana ga mutuncin marubuta da ake yi wa kallon malaman al’umma, ta yaya ka ke ganin za a tsaftace alƙaluman matasan marubuta?

To, maganar tsaftace rubutu abu ne mai yiwuwa amma idan aka yi niyya, marubutan batsar nan yara ne ƙanana masu tasowa da kawai sha’awar rubutun suke yi don wata buƙata tasu, duk da na ga a yanzu an samu sauƙi kwarai.

Amma babbar hanya ita ce shirya bita a kan rubutu duk sati tun da Allah Ya kawo zamanin soshiyal midiya, yana da kyau a zaurukan da ake da su a manhajar WhatsApp don haɗin kan marubuta a dinga kiran masana duk sati suna faɗakar da marubuta a kan illar rubutun batsa.

Marubuci ya tuna akwai ranar da zai yi nadamar abin da ya rubuta yayin da shekaru suka ja ko tsufa ya riske shi, zai ji kunyar ‘ya’yansa su gani su karanta. Sannan in dai marubucin na gaske ne ba zai yi rubutun batsa ba.

Bayan harkar rubutun adabi, ta wacce hanya marubuta za su ba da gudunmawa ga cigaban harkokin al’umma a siyasance da sha’anin tafiyar da mulki?

Akwai abubuwa da yawa da suka kamata a lura da su, marubuci fa ba iyaka rubutu ya tsaya ba, rayuwar al’umma yana hannunsa sai yadda ya so su zama za su zama. In kuwa haka ne akwai buƙatar marubuta su shiga al’amuran siyasa kace-kace ba raragefe ba.

A samu wasu su fito takara, wannan zai sa su motsa rayuwar gabaɗaya, idan za su iya canza tunani ta hanyar rubutu kaɗai ina kuma ga a ce ragamar al’umma ta zahiri tana hannunsu?

A wannan zamanin rubutu da marubuta na cikin wani hali, na farko akwai karancin masu karatu, na biyu akwai ƙarancin jari ga marubuta haka akwai karancin martaba daga mutane, har yanzu ba a ɗaukar rubutu (musamman na Hausa) da daraja dole sai gwamnati da ƙungiyoyin sa kai sun saka jari wajen samar wa da marubuta wani gata musamman ta hanyoyin tallata littattafai na zamani da shirya musu bitoci, kai har da ma ba su muƙamai a gwamnati domin bayar da shawarwari.

Ban da ƙungiyoyin marubuta da kuɗaɗe domin mafi yawansu sun durƙushe. Ko lokacin da suke a tsaye babu wata ƙungiya ta marubuta da take da tsayayye kuma wanzajjen ofis balle a je ga motar hawa.

Wanne tallafi marubuta ke buƙata daga gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu, a ɓangaren yaɗa ilimi da wayar da kan jama’a?

A wannan gaɓar ina kira ga gwamnati musamman sabuwar nan dake hawa da su daɗa martaba ilimi musamman na yara domin ilimi ne jigon rubutu da karatu. Domin ba a rubutu ko karatu da jahilci.

Wacce shawara za ka bai wa marubuta don bunƙasa adabi da harshen Hausa?

Shawarar da zan ba su ita ce rubutu a kan al’adar Malam Bahaushe, har yanzu muna fama da ƙarancin irin waɗannan labaran, sai ka ga labarin Hausa amma rayuwar irin ta Turawa ce zalla, sannan Hausar ma sai ka ga ana amfani da Hausar baka, wanda hakan ya fara tasiri a cikin Hausawan yanzu hatta a finafinanmu. Sannan akwai ƙarancin bincike yayin rubutun, muna da Malamai a jami’o’inmu da a shirye suke su ba da duk wata gudummawa daga wurinsu, za su jiɓinci lamurran marubuta to, a kusance su mana. Sannan akwai iyayenmu a rubutun nan da Yayyanmu. Sannan a dinga hausantar da sabbin kalmomi musamman na wani yaren, a tambayi malamai masana Adabin Hausa kai da kai.

Ba mu labarin irin nasarorin da ka samu a irin fasahohin da ka ke da su?

Na samu kyaututtuka, mafi yawa na gasar rubutu ne da akan saka lokaci-lokaci. Mafi girman kyautar da na samu ita ce wadda aka ba ni a Jami’ar Jihar Kano ta KASU wadda na zo a matsayi na biyu, an ba ni kyautar kuɗi da na ji daɗin su domin ana gab da ɗaurin aurena na samu wannan nasarar.

Sai kuma kyautar da na samu a gasa daban-daban da na lashe a matsayi na ɗaya, waɗansu a ba ni kuɗi da littattafan nazari yayin da waɗansu kuma akan ba ni kambun girmamawa, an sha karrama ni a tarurrukan marubuta saboda gudunmawar da nake bai wa Adabi. A nan ina jinjina ga ƙungiyata ta HAF (Hausa Authors Forum) saboda duk abin da na samu a rubutu ta zame mini tsani, na ƙaru da ita sosai. Kyauta ta baya-bayan nan ita ce wadda aka ba ni a yayin nasara a gasar waƙa da aka yi a Kano akan fyaɗe wadda na lashe a matsayi na ɗaya. Na gode wa Allah.

Wanne abu ne yake faranta maka rai game da rayuwar marubuta?

Haɗin kai da raha da wasa da dariya. Ina jin daɗi duk sadda na haɗu da marubuci marubuta, sai in ji bana son mu rabu, kuma hirata da su ba ta yankewa.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?

Ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka.

Mun gode.

Ni ma ina godiya.