Gwamnatin Kano ta horar da masu sana’ar sayar da kayan noma

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A makon da ya gabata ne shirin bunqasa harkar noma da kiwo na Jihar Kano da ake kira da KSDP ya horas da masu sayar da kayan noma, waɗanda suka haɗa da maganin ƙwari da na feshi, hanyoyin da za su bunƙasa sana’oinsu.

Horarwa an yi ta ne a shiyyoyi daban-daban na faɗin jihar, inda maharta taron suka fito daga qananan hukumomin jihar daban-daban.

A yayin bitar, an ja hankalin mahalarta taron hanyoyin da za su bi, domin su kare amfanin gona ta hanyar sayar da ingantattun kaya, domin su ne ginshiƙi wajen tabbatar da lafiyar al’umma.

Malam Abdurrahman Baba Saje, shi ne jami’i mai lura da bunƙasa kasuwanci a ofishin Sasakawa Global 2000. Ya buƙaci mahalarta taron da su tabbatar sun yi rijista hukumar CAC, domin yin hakan zai taimaka musu tare da inganta harkokin kasuwancin su.

Haka zalika ya nuna musu dabarun yadda ake aiwatar da kasuwanci a zamanance ta hanyar bin tsare-tsarensa.

Mahalarta taron sun baiyanna jin daɗinsu tare da jaddada goyon bayansu ga shirin bunƙasa noma da kiwo na jihar Kano, wanda hukumar Sasakawa Global 2000 ta ke aiwatarwa.

Sun kuma tabbatar cewa, a shirye suke wajen ganin sun aiwatar da abinda suka koya, gami da koyarwa ga ragowar ’yan uwansu masu sana’a irin tasu.