Albashin ‘yan majalisa ya yi matuƙar ƙazanta – Isyaku Ibrahim

Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD 

Ɗimbin kuɗin albashin da ‘yan majalisun ƙasa suke ƙarawa kansu yana zama cin amana ne ga jama’a masu kaɗa ƙuri’a, don ya yi matukar ƙazanta.

Alhaji Isyaku Ibrahim, wanda shine Tsohon Ma’ajin rusasshiyar Jam’iyyar NPN a Jamhuriya ta Biyu, watau a zamanin gwamnatin Marigayi Shehu Shagari, ya shaida wa Jaridar Manhaja cewa, “Babban cin amanar ƙasar Nijeriya ne, ‘yan majalisa da talakawa suka wuni da yunwa da wahala suka zaɓe su, amma suna ta ƙara wa kansu zunzurutun albashi.

“Bugu da ƙari, sun ƙi jajircewa don ganin an biya talakawa masu aikin albashi mafi ƙarancin albashi na Naira dubu talatin kacal.

“Na fara siyasa tun kafin a ba Nijeriya ‘yancin kanta, burin mu shine a samawa talaka sauƙin rayuwa ba akasin haka ba.

“Haka aka yi a zamanin mulkin Marigayi Firayi Minista Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa, da Sardauna Ahmadu Bello da sauran su.

“A mulkin Marigayi Shehu Shagari an samar da gidaje da abinci don jama’a”, a cewar dattijon.

Alhaji Isyaku Ibrahim ya ƙara da cewa, duk wanda ya yi bibiyar albashin ‘yan majalisu, ya san a da kuɗaɗensu a ƙayyade suke, amma abin ban haushi sai ‘yan majalisu daga 1999 har ya zuwa yanzu, ba abinda suke sai cin duddugen ƙasa, suna yi wa doka karan-tsaye suna ta ƙarawa kansu albashi ba gyaira, ba sabab.

Dattijon ya shawarce da cewa, wannan kwamacala ita ta sanya talakawa suka fara daina fita zaɓuɓɓukan ƙananan hukumoni da aka gudanar a jihohin Ikko da Kaduna da sauran su.

Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce mafita guda ɗaya ce, “Ɓangaren zartaswa, da ta shari’a da su hana ɓangaren majalisa yin gaban kansu don a tabbatar da ɗorewar mulkin farar hula ta hanyar bin doka ba sani ba sabo, don talakawa su rinƙa fita yin zaɓe ɗungurungun.