Pantami ya yi wuf da Shugaban EFCC, Abdurrasheed Bawa, lokacin da jiri ya kwashe shi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotannin da Jaridar Manhaja ta samu ya sun nuna cewa, a lokacin da jiri ta kwashi Shugaban Hukumar Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Nijeriya Ta’annati, wato EFCC, Malam Abdurrasheed Bawa, Ministan Sadarwa, Sheikh Isah Ali Pantami ne ya yi wuf ya kawo masa agaji.

Bayanan sun tabbatar da cewa, Abdulrashid Bawa, ya yanke jiki ya faɗi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja ran Alhamis da ta gabata.

Lamarin dai ya faru ne lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen wani taro a fadar shugaban ƙasar. Kwatsam sai ya daina magana ya yanke jiki ya faɗi, daga nan aka yi awon gaba da shi zuwa asibiti.

Wasu manyan mutane ciki har da Ministan Sadarwar Nijeriyar Isah Ali Pantami, sun kasance da shi zuwa wani ɗan lokaci.

Shugaban na hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa dai yana bayyani ne kan wani mutum da aka kama da layukan waya 116 yana damfarar mutane. Kwatsam a daidai lolacin sai ya daina magana ya yanke jiki ya faɗi, inda nan da nan aka wuce da shi asibiti, ciki har da taimakon Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami.

Sai dai kuma awanni kaɗan bayan afkuwar wannan al’amari, hukumar EFCC ta fitar da sanarwa ga manema labarai cewa, Shugaban EFCC ɗin ya samu sauƙi, har ma ya koma bakin aiki.

Amma a cikin takardar manema labarai da hukumar ta fitar ba ta yi wani ƙarin haske ba kan abin da ya sa Bawa ya shiga yanayin rashin lafiya.