Wata matashiya ta shayar da ‘ya’yan mijinta guba a Yobe

Daga AMINA YUSUF ALI

‘Yan sanda a jihar Yobe sun cafke wata mata mai shekaru 22 a kan zargin kashe ‘ya’yan mijinta su 3.

Matar mai suna Khadija Yakubu, ta sanya wa ‘ya’yan mijinta su huɗu guba a garin Malariya Huta, da ke garin Potiskum ɗin Jahar Yobe.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkareem, ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya ƙara da cewa, wacce ake zargin ta shayar da ‘ya’yan mijinta na wajen uwargidansa su huɗu shayi wanda yake ɗauke da guba a ciki.

Inda aka binne yara ukun da suka rasu

Yaran mijin nata su ne, Umar Haruna, mai shekaru 12; sai Maryam Haruna, mai shekaru 11; Ahmed Haruna, mai shekaru 9, Sai mai shekaru 7, Zainab Haruna.

Bincike ya nuna cewa, a ranar Juma’a bayan yaran su huɗu sun sha shayin wanda matar ubansu Kahadija Yakubu ta zuba wa guba, an garzaya da su ya zuwa asibiti. Inda 3 daga cikinsu suka ce ga garinku a yayin da suke tsaka da amsar taimakon asibiti. Shi kuma guda daga ciki da ya rage ya fita daga hayyacinsa kuma yana jin jiki.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan ya bayyana cewa, hukuma za ta ci gaba da tsare wacce ake zargin, yayin da za a ci gaba da gudanar da binciken. Sannan a gurfanar da ita gaban kotu daga bisani.