Gwamnatin Kano ta yi ta’aziyyar Babban Malami na Madabo

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Cikin kaɗuwa da jimami Gwamnatin Jihar Kano ta samu labarin rasuwar Malam Kabiru Ibrahim, Babban Malami na Madabo.

Wanda fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa ilimin addini da koyar da kyawawan ɗabi’u, abin da ya shafi al’umma da dama a Kano da wajen ta.

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin Malam Kabiru Ibrahim, wanda aka bayyana a matsayin ginshiƙin ilimi, tawali’u, da zaman lafiya. Karatuttukansa da shawarwarinsa sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ɗabi’a da ruhin addini a cikin al’umma.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin cikin gida ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa marigayin bai tsaya kawai a matsayin malamin addini ba, har ma jagora ne wajen tarbiyyar matasa, wanda kullum yake kira da a riƙa neman zaman lafiya, biyayya, da mutunta kowa.

Rasuwarsa ta bar babban giɓi a fagen koyar da ilimin addini, ba kawai a unguwar Madabo ba, har ma a faɗin jihar Kano da ma ƙasar baki ɗaya.

Gwamnatin Jihar Kano tana mika ta’aziyyarta ta musamman ga iyalan marigayin, almajiransa, abokansa, da dukkan al’ummar Musulmi, tana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuransa, ya karɓi ayyukansa na alheri, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdaus.

Gwamnati da al’ummar Kano baki ɗaya suna cikin wannan juyayi, wanda ba wai na iyalan marigayin kaɗai ba ne, har ma na jihar gaba ɗaya, la’akari da gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimin addini da cigaban al’umma.

A ƙarshe, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi kira ga jama’a, musamman matasa, da su yi koyi da kyawawan halayen marigayin — musamman tsoronsa ga Allah, sauƙin hali, da jajircewarsa wajen hidima ga ɗan Adam.

By ukarofi