Gwamnatin Kano za ta ci gaba da tafiya kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyi

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU aKano

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da tafiya kafaɗa da kafaɗa da duk wata kungiya da ke da manufar bunƙ asa rayuwar al’umma a faɗin jihar. 

Darakta Janar ta Hukumar Bincike da Adana Bayanai ta jihar, Dr. Asma’u Jibrin, ce ta bayyana hakan yayin da take karɓar lambar girmamawa daga ƙungiyar Kwankwasiyya Media Production, tare da wasu masu bai wa Gwamnan Jihar shawara, a Ma’aikatar Yaƙi da Talauci da Jinƙan Al’umma, a ranar Litinin da ta gabata.

Dr. Asma’u Jibrin ta bayyana cewa ƙungiyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’umma, shi ya sa gwamnatin jihar ta sha alwashin tafiya tare da su a dukkan shirye-shiryenta na inganta rayuwar jama’a. Ta ce Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya fahimci irin gudummawar da ƙungiyoyi suka bayar a lokacin yaƙin neman zaɓe, wanda hakan ya sa gwamnati ke tantance ƙungiyoyi domin tallafa musu.

Ta ƙara da kira ga ƙungiyoyi da su ci gaba da mara wa gwamnati baya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, domin cimma manufofin cigaba a jihar. Haka kuma ta nuna godiyarta ga mambobin ƙungiyar Kwankwasiyya Media Production bisa wannan karramawa, tana mai cewa hakan zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ruɓanya ƙoƙ ari domin amfanin al’umma.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar Kwankwasiyya Media Production, Kwamared Abubakar Hussaini Aramma, ya ce sun zaɓi karrama jami’an ne bisa la’akari da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa ƙungiyoyi da al’umma a jihar. Ya bayyana cewa an gudanar da bincike mai zurfi kafin bayar da lambar yabon, yana mai fatan hakan zai ƙara musu ƙ wazo wajen taimaka wa Gwamnatin Jihar Kano don samar da ingantattun ayyukan cigaba.

Da yake jawabi a madadin waɗanda aka karrama, Hon. Muttaka Sani Gaya, Mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin bunƙasa kungiyoyi, ya bayyana farin cikinsu da wannan karramawa, yana mai cewa babbar nasara ce a rayuwarsu. Ya kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin goyon bayan da yake bai wa ƙungiyoyi a jihar. 

Waɗanda aka karrama sun haɗa da Hon. Muttaka Sani Gaya, Hon. Kabiru Hussaini Zuwaciki, tsohon Sakataren Shirye-shirye na NNPP, da Dr. Asma’u Jibrin. Taron ya samu halartar Sarkin Yaƙin Gaya Alhaji Sa’idu Madaki Gaya, Mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin Majalisa Balarabe Bunkure, daraktoci da ‘yan siyasa maza da mata.

By ukarofi