Dagacin Gama, Alhaji Rabiu Isyaku, ya cika shekaru 25 a kan mulki

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An gudanar da bikin cika shekaru ashirin da biyar da naɗa Dagacin Gama, Alhaji Rabiu Isyaku, a kan mulki, a fadarsa da ke garin Gama, ƙaramar hukumar Nasarawa, a ranar Lahadi.

Dagacin Gama ya bayyana godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa ba shi damar kai wannan matsayi na shekaru 25 yana jagorantar al’ummarsa. Ya ce wannan nasara babbar ni’ima ce da ke nuna rahamar Allah da goyon bayan al’umma.

Alhaji Rabiu Isyaku ya bayyana farin cikinsa bisa yadda ake zaman lafiya da jituwa a yankin Gama duk da kasancewar al’umma masu kabilu daban-daban. Ya ce tun daga masarautar Kano, hakimai, masu unguwanni, har zuwa wakilan gwamnatoci na baya da na yanzu a matakin ƙaramar hukuma da jiha, ana gudanar da mulki cikin fahimta da haɗin kai, ba tare da samun wata saɓani mai tsanani ba.

Ya yabawa masu unguwanni, malamai da duk masu ba shi shawarwari, yana mai cewa irin waɗannan shawarwari ne ke taimaka masa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa. Haka kuma ya gode wa ƙungiyar Gama ƙarƙashin jagorancin Farfesa Muhammad Shehu Husain, da dukkan masu ba da gudummawa wajen cigaban garin, tare da jami’an ‘yan sanda na Gwagwarwa da ke tabbatar da tsaro tun daga hawansa mulki.

Dagacin ya tuno da Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, inda ya ce a zamaninsa aka naɗa shi Dagacin Gama. Ya ƙara da cewa ya yi aiki a ƙarƙashin sarakuna uku, kuma a halin yanzu yana ƙ arƙ ashin jagorancin Khalifa Muhammadu Sanusi, wanda yake biyayya gare shi tare da aiwatar da dukkan umarnin da ke zuwa daga Masarautar Kano da ofishin Hakimi zuwa ga al’umma.

A ƙarshe, Alhaji Rabiu Isyaku ya gode wa hakimai, wakilai da masu unguwanni, waɗanda ke raye da waɗanda suka rasu, bisa irin goyon bayan da suka ba shi tun daga lokacin naɗa shi. Ya kuma roƙi gafarar al’ummar yankin, yana mai cewa duk wanda ya ɓata masa rai ba tare da sani ba, ya yafe masa, haka nan shi ma ya yafe wa kowa.

By ukarofi