Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An bayyana kyawawan ɗabi’u da halayen marigayi tsohon Na’ibin Limamin Dawakin Kudu, Ustaz Malam Kabiru Yahaya, a matsayin abin koyi ga al’umma, musamman matasa masu tasowa.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Alhaji Salisu Abdullahi Dawakin Kudu, Mukaddamin Hakimin Gundumar Darmanawa, a sakon ta’aziyyarsa bayan rasuwar malamin, wadda ta faru a ranar Juma’a da ta gabata bayan doguwar jinya.
Alhaji Salisu ya bayyana rasuwar Malam Kabiru a matsayin babban rashi ga garin Dawakin Kudu, yana mai cewa gudunmawar da marigayin ya bayar wajen yaɗa addinin Musulunci da tarbiyyar al’umma ba za a taɓa mantawa da ita ba. Ya ƙara da cewa halayen marigayin sun yi kama da na Manzon Allah (SAW) ta fuskar gaskiya, haƙuri da kyakkyawar mu’amala.
A cewarsa, “Malam Kabiru Na’ibi shi ne ya koya min yadda zan yi sallah, karatun Alƙur’ani, da kuma yadda zan bautawa Allah da son ManzonSa. Malami ne da ya gina mutane ta hanyar tarbiyyar addini. Allah ya saka masa da Aljannar Firdausi.”
Marigayi Malam Kabiru Yahaya ya rasu yana da shekaru 87, ya bar mata hu u, ‘ya’ya 28, da jikoki 113. Shi ne malami na biyu da ya fara buɗe makarantar Islamiyya a ƙofar gidansa, wadda daga bisani ta bunƙasa zuwa makarantar firamare, sannan ta samu sashin sakandare a Dawakin Kudu.
Kafin rasuwarsa, ya kasance Na’ibin Limamin Babban Masallacin Juma’a na Dawakin Kudu ƙarƙashin jagorancin Marigayi Sheikh Tijjani Umar, wanda ya rasu shekaru uku da suka gabata. Bayan rasuwar Sheikh Tijjani, an naɗa ɗansa, Umar Tijjani Umar, wanda daga bisani ya yi murabus.
