Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Ranar 15 ga watan Janairu na kowacce shekara rana ce da aka ware domin tunawa da tsofaffin sojoji, wato ‘Yan Mazan Jiya, waɗ anda suka fafata a Yaƙ in Duniya na Farko da na Biyu, Yaƙin Basasar Nijeriya, da kuma waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu a fannonin tsaro domin kare martabar ƙasa.
Tun da fari, ana gudanar da wannan biki ne a ranar 11 ga watan Nuwamba, wadda aka fi sani da Poppy Day (11-11), musamman a ƙasashen Turai. Sai dai sakamakon tarihi da kuma kawo ƙarshen yaƙin Basasar Nijeriya a ranar 15 ga Janairu, 1970, aka mayar da ranar zuwa 15 ga watan Janairu a duk faɗin Nijeriya.
A jihar Kano, an gudanar da bikin tunawa da ‘Yan Mazan Jiya a sabon filin taron tsofaffin sojoji da ke Dotsa, a kan titin Kano zuwa Zariya. Taron ya samu halartar jami’an sojoji na ƙasa, ruwa da sama, da kuma tsofaffin dakarun da suka yi ritaya.
Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban ƙungiyar tsofaffin sojoji a Kano (AWO), Kabiru Isyaku mai ritaya, ya bayyana cewa ranar tana da matuƙar muhimmanci a gare su, domin tana basu damar tuna ‘yan uwansu da suka rasa rayukansu yayin aikin kare ƙasa. Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ƙara duba halin da wasu tsofaffin sojoji ke ciki, musamman matan da aka bar musu marayu, ta hanyar saka su cikin shirye-shiryen tallafi da gwamnati ke aiwatarwa.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya wakilta, ya jinjina wa tsofaffin dakarun bisa sadaukarwar da suka yi. Ya tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba su goyon baya da duk wani tallafi da suke buƙata.
Wasu daga cikin ‘Yan Mazan Jiya da aka zanta da su, ciki har da Manjo Habibu Sadau Ibrahim (mai ritaya) da Kaftin Bello Muhammad Mai Gaskiya (mai ritaya), sun bayyana ranar a matsayin tarihi mai matuƙar muhimmanci, tare da yin kira ga dakarun da ke kan aiki da su yi koyi da sadaukarwar da tsofaffin sojoji suka yi.
