Daga RABI’U SANUSI
Kwamishinar Ma’aikatar Yawon buɗe ido da Raya Al’adu ta Jihar Kano, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano ta bayyana cewa nan bada jimawa ba Gwamna Abba Kabir Yusuf zai gwangwaje marayu da yaran da suke da ƙarancin gata domin su kai ga gaci a rayuwarsu da kuma samun ilimi kamar kowane yaro.
Hajiya Aisha Saji ta bayyana hakan ne lokacin da Kungiyar Mata ma su Yaƙin neman Ƴancin Matan da aka mutu aka barsu da Marayu (UBWA), reshen jihar Kano suka kai mata ziyara a ofishinta.
Ta bayyana cewa duk nasarar da ake samu ta ta’allaƙa ne ta dalilin da Gwamna Abba ya ke bayarwa kyauta domin su ma su ci moriyar dimokuraɗiyya.
Saji Rano ta yaba wa wannan ƙungiyar da irin ƙoƙarinta na ganin matan da mazajensu suka mutu suka bar su da ƙananan yara sunji daɗi kamar waɗanda ba su ba.
Ta kuma tabbar masu da ba su goyon baya a kowane lokaci duk da cewa ta samu canjin ma’aikata amma buri ne na gwamna ya ga an tallafawa marassa ƙarfi.
Tun a farko shugabar tawagar, Hajiya Rabi Fagge ta bayyana cewa ta zo ma’aikatar ne domin yabawa kwamishinar na irin ƙoƙarin da take yi da jajircewa akan cigaban mata da yara marayu musamman a lokacin da take ma’aikatar da ta baro sannan ta bata kanbun girmamawa.
Bayan miƙa mata kambun yabawar ne, kwamishiniyar ta bayyana cewa wannan kambun yabo za ta miƙa shi ga Mai Girma gwamna domin shi ya ke zaburar da su wajen samun nasarori a Jihar Kano.