Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta amshi magunguna daga wata hukuma tallafawa da magunguna a Detroit da ke ƙasar Amurka.
Jami’in yaɗa labarai na gwamnan jihar malam Kuala Muhammad ya faɗi haka a wata takardar sanarwar da ya sanya hannu.
Kawo magungunan, ya biyo bayan ziyarar da gwamna Dikko Raɗɗa ya kai a cibiyar hukumar a kwanakin baya inda ya samu ganawa da shugaban hukumar Mr George Samson da sauran jami’an hukumar.
Gwamnan ya gabatar da buƙatar sa ga hukumar na ganin ya samar wa al’ummar Jihar Katsina ingantaccen tsarin kiwon lafiya,ya kuma shaidawa Mr Samson da bayanai da gwamnatin jihar ta tattara kan halin kiwon lafiya a jihar.
Akan haka ne shugaban hukumar ya tabbatar wa da gwamna Raɗɗa cewa hukumar za ta tallafawa wa jihar Katsina da magungunan na kimanin Dalar Amurka miliyan 10.
Yanzu haka har wasu kayan magungunan sun iso jihar, sauran sun baro Legas suna kan hanyar zuwa Katsina.
Haka kuma shugaban hukumar yayi alƙawarin taimakawa Jihar Katsina da wasu na’urorin gwaje gwaje da bada horo ga jami’an kiwon lafiya.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan haɗin gwiwa da hukuma a matsayin a matsayin ƙudirin gwamnatin sa na dai-dai ta tsarin kiwon lafiya a jihar.