Gwamnatin Katsina ta gurfanar da masu cin zarafin mata a kotu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta gurfanar da masu cin zarafin mata da bil’adama a babban Kotun Tarayya dake jihar.

Kwamishinar Shari’a ta jihar, Barista Fadeela Muhammad Dikko ta shaida wa manema labarai haka bayan kammala zaman kotun.

Ta ce bayan da Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a dokar hukunta masu laifin aikata fyaɗe da cin zarafin bil’adama a jihar, Ma’aikatar Shari’a ta kafa kwamitin ko-ta kwana inda ba tare da ɗaukar tsawon lokaci ba kwamitin ya gano shari’a guda 50.

Kwamishinar ta ƙara da cewa a yanzu haka Ma’aikatar tana da shari’a guda 40 da zata gabatar a kotu.

Ta ce a baya mutane suna ganin masu aikata ire-iren laifuffukan sun fi ƙarfin Shari’a, “amma yanzu ku yan jarida kun gani da idanunku mun gabatar da irin waɗannan miyagun mutane a kotu.

Fadeela ta kuma bayyana cewa babu wanda yafi ƙarfin hukuma, saboda haka duk wanda aka kama da laifin aikata fyaɗe da cin zarafin bil’adama zai fuskanci Shari’a.