Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanarda dakatar da gini da duk wata hulɗa ta saye da Sayar da fili ko gini a kan sabon titin da gwamnati ke ginawa,wanda zai zagaye birnin Katsina ta Gabas. Wato Eastern by-pass.
Wannan dakatarwar ta shafi wuraren da suka fara daga titin zuwa Dutsinma, kusa da Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua zuwa garin ‘Yanɗaki da ke Ƙaramar hukumar Kaita.
Kwamishinan ma’aikatar Ƙasa da tsare-tsare ta Jihar Katsina Dr.Faisal Umar Kaita ya sanar da hakan a lokacin da ya ke ƙaddamar da bayar da chakin Kuɗaɗen diyya ga waɗanda za a yi amfani da wurarensu domin gina tagwayen hanyar mai tsawon kilomita 24.1.
Dr.faisal Umar Kaita yace duk mai buƙatar yin wata hulɗa da ta shafi wani ɓangare na wannan titin,dole sai an tuntubi hukumar tsara birane ta Jihar Katsina don neman izni,don gwamnati ta yi tsari na musamman na yarda ta ke buƙatar wuraren su kasance.
A cewar Kwamishinan sun samar da tsarin da zai magance cunkoson da
unguwanni za su fuskanta a dalilin rashin bin Ƙa’idojin da suka dace,don haka ba za a sa ido ba a maimaita yar gidan jiya ba.
Dr.Faisal Kaita wanda ya bayyana cewar kimanin mutane 981 ne suka amfana da kuɗi Naira miliyan 528,434,202,a matsayin Kuɗaɗen diyyar wurarensu, ya kuma tabbatar da cewar gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta kashe kuɗi sama da Naira Miliyan dubu huɗu,wajen biyan wurare daban-daban da ta amsa daga hama’a don ayyukan raya Ƙasa,tun da ta fara aikin sabunta Jihar Katsina.