Gwamnatin Katsina ta haramta aikace-aikacen ’yan sa-kai

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari ta haramta ayyukan ‘yan  sa kai a duk faɗin jihar.

Bayanin haka na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai ba wa gwamnan jihar shawara a kan harkokin tsaro Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina.

Kamar yadda takardar ta bayyana dakatar da aikace-aikacen ‘yan sa kai ɗin ya biyo bayan kashe-kashen mutane da ake yi ba gaira babu dalili a jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewar dokar ta fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu na wannan shekarar da muke ciki.

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin Jihar Katsina ta aminta ne kawai da aikin ‘yan ƙungiyar sintiri wanda suke a ƙarƙashin kulawar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da masu riƙe da masarautu a jihar.

A cewar sanarwar daga yanzu gwamnati ta bayar da umarni a kan cewar duk wani da ake zargi da ayyukan ta’addanci da aka kama a hannanta shi ga jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

Tuni dai gwamnatin jihar ta bai wa jami’an tsaro umarni akan su kama duk wani wanda aka kama da yunqurin bijire wa dokar da sunan yana aikin sa kai.

A ɓangare ɗaya kuma wasu ƙungiyoyin fararen hula sun nuna adawarsu bisa wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka, inda suka bayyana shi da cewa sha’anin tsaro zai ƙara taɓarɓarewa a jihar tare da tunatar da gwamnatin cewar a baya gwamnan jihar ya buƙaci al’umma akan su tashi tsaye don kare kawunan su daga hare-haren ‘yan bindiga a wani taron manema labarai da shugaban gamayyar ƙungiyoyin fararen hula Abdulrahman Abdullahi ya fitar ya bayyana cewar bai kamata a saka wannan doka ba a daidai lokacin da ‘yan ta’adda ke ci gaba da ta’adi a wasu yankunan ƙananan hukumomin jihar kasancewar ‘yan sa kai suna taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ɓarayin daji.