Gwamnatin Katsina ta kashe Naira biliyan 27 kan ilmi a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A ƙoƙarin ta na bunƙasa sha’anin ilimi, gwamnatin Jihar Katsina daga hawan ta zuwa yanzu ta kashe Naira biliyan 27 wajan ilimin firamare, sakadanre da na gaba da sakandare a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Farouk Lawal Joɓe ya bayyana haka a hira da yayi da manema labarai a Katsina.

“A cikin wannan adadi, gwamnatin jihar ta kashe fiye da Naira biliyan tara a fannin ilimin firamare ƙarƙashin hukumar ilimin bai ɗaya (SUBEB)”Mataimakin gwamnan ya ce.

Ya ce gwamnatin jihar Katsina ta gina ɗakunan karatun ɗalibai guda 160 da gidajen Malamai guda 20 da rijiyar burtsatse 81 tare da wurin bahaya 46.

Haka kuma Farouk Joɓe ya sanar da gyara wasu ɗakunan karatu 258 da kujeru da teburin malamai 612 da kuma kujerun zama na ɗalibai guda 14,602.

“Gwamnatin jihar ta sayi isassun littafai da sauran kayan karatu da suka haɗa da kwamfuta da fitila mai amfani da hasken rana da ta raba wa makarantun da ke faɗin jihar”Farouk Joɓe ya ce.

Ya kuma sanar da cewa malamai 274,816 suka sami horo daban daban kan sanin makaman aiki a jihar.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta kashe Naira biliyan 6.8 wajan ilimin sakandire a jihar.

“Sun kuwa haɗa da gina tare da gyara wasu makarantu da samar da kayan karatun kimiyya da fasaha, da kuma littafai da biyan bashi na ‘yan kwangila”inji joɓe.

Ya ce gwamnatin jihar ta maido da wutan lantarki a jami’ar Umaru Musa Yar’adua da samar da fitillu masu amfani da hasken rana a jami’ar.

“Gwamnatin Dikko Raɗɗa ta kuma samar da ababe na more rayuwa a sauran mayan makarantu mallakan gwamnatin jihar”Joɓe ya faɗi haka.

Ya jaddada ƙudirin gwamnatin jihar ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa na cigaba da baiwa ɓangaren ilimin kulawar da ya dace.

By ukarofi