Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Katsina ya magantu game da batun rufe makarantu a lokacin watan Ramadana wanda ya alaƙanta matakin da cewa yunƙuri ne na bai wa harkar ibada da cigaban ilimi muhimmanci.
Ma’aikatar kula da ilimi a matakin farko a jihar Katsina ta ce akwai dabaru da ta aiwatar da ba za su kawo wa harkar ilimi wani cikas ba sabili da wannan hutu.
Ma’aikatar ta ce ta yi la’akari da tsananin zafin rana wanda abu ne da aka san yankin Arewa da har kuma a jihar Katsina.
“Haka kuma gwamnati na sane da irin ƙalubalen da malamai da ɗalibai ke ciki a yayin wannan wata mai albarka wanda hakan ya sa ma’aikatar samar da wata dabara ta sauƙaƙa koyo da koyarwa da kuma ibada,” inji Sani ɗanjuma Suleiman, jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar wanda ya bayyana hakan a ranar Talata.
A yayin da yake magana a kan matakin gwamnatin, ya ce, “manufarmu ita ce bai wa ɗalibai musamman waɗanda suke ajin ƙarshe damar shirya wa jarrabawarsu.
“Ma’aikatar ta shirya wa ɗaliban da ke babbar sakandare ajin ƙarshe aji na da ke shirin jarrabawa aji na musamman a makarantun gwamnati da masu zaman kansu a unguwanninsu,” inji Suleiman.
Sannan ya tuna wa iyaye da al’umma bakiɗaya cewa akwai dokar da ta ba da izinin rufe makarantu bakiɗaya a lokacin watan Ramadana.
“La’akari da damuwarsu da wasu masu ruwa da tsaki a Nijeriya suka nuna da yaɗa da ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), ma’aikatar na son sanar da al’umma cewa akwai karatu na musamman da za a fara gudanarwa a ranar 3 ga watan Maris ɗin 2025 wanda aka tsara domin sauƙaƙa wa ɗalibai da malamai a wannan wata ta la’akari da yanayin da ake fama da shi.
“Gwamnatin Dikko Umaru Raɗɗa ta himmatu wajen samar da yanayin karatu mai kyau ba tare da la’akari da bambancin addini ba da kuma tabbatar da ingancinsa.
“Gwamnati na ƙara kira ga makarantu da su bi waɗannan ƙa’idoji da aka shimfiɗa domin tabbatar da an taimaka wa ɗalibai,” a cewar sanarwar.
