
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta da bubbar murya zargin da wani Bashir Kurfi ya yi a wata kafar yaɗa labarai cewa ta dauki nauyin shugabannin ‘yan bindiga zuwa aikin Hajjin da ya gabata.
A wata takarar sanarwa ɗauke da sa hannun kwamishinan harkokin cinkin gida da tsaro, Dr Nasiru Mu’azu Danmusa ya sanya wa hannu, gwamnatin katsina ta bayana zargin da kurfi yayi a matsayin karya da sharri da kokarin yaudarar alummar jihar katsina da Kuma yunkurin kawo cikas a kokarin da gwamnati da jami’an tsaro ke Yi na kawo zaman lafiya a jihar.
Dr Danmusa ya nuna takarcin sa cewa wannan zargi ya zo daidai lokacin da gwamnati da jami’an tsaro ke samun nasara a yaki ta taadanci da sauran masu aikata laifuka a fadin jihar.
Haka Kuma gwamnati ta nuna damuwar ta yadda wasu mutane domin son zucciya suka siyasartar da harkar tsaro domin biyan bukatar kansu, acewar Dr Nasiru.
Kwamishinan sai ya kalubalanci Mai wannan zargi da ya fito da shaidu akan zargin da yayi ko Kuma gwamnati zata dauki matakin doka domin ta kare mutuncin kanta Kuma masu wannan zargi su girbi abinda suka shuka.
Yayi Kira ga alummar jihar katsina da su nisanta kansu daga irin wadannan karairayi su cigaba da ba gwamnati , jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki goyon baya a bisa kokarin da suke ba dare ba rana domin kawo zaman lafiya a fadin jihar.
