Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wannan aikin madatsar ruwa mataki na farko na da nufin samar da ruwan sha ga al’ummar ƙananan hukumomin Dutsinma, kankiya, Charanchi, Rimi da Ɓatagarawa.
Majalisar zartarwar Katsina ta amince da haka a zaman ta na karo na 15 ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa.
Haka kuma majalisar ta amince da gyara kasuwanni da zamanantar da wasu zaɓaɓɓu a ƙananan hukumomi 34 da inganta guda 2 a shiyar Katsina, Funtua da Daura zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa.
Gwamnatinn Katsina ta kuma amince da daftarin kula da yan gudun hijira na jihar da tsare-tsaren aiwatar da shi domin samun ingantaccen hanyoyin magance matsalolin ‘yan gudun hijira.
Harwala yau majalisar zartarwa ta amince da tallafawa mata masu ƙananan sana’o’i guda 14,450 domin inganta tattalin arzikin jihar musamman na mutanen karkara.
Duk dai a zaman majalisar zartarwa,ta amince tsare-tsaren raba filaye a yankin tattalin arziki na musamman (GREEN ECONOMIC ZONE) don hanzarta bayar da filaye ga masu zuba jari.
Haka kuma gwamnati za ta sake duba sabuwar doka kan makarantun firamare da na sakandare masu zaman kansu bisa buƙatar da ƙungiyar makarantun NAPPS reshen jihar Katsina ta yi.
Majalisar zartarwa ta amince da gina gidaje da kuma tsarin rarraba filayen masu gadi a kan sabuwar hanya ta wajen gari watau Eastern bypass a cikin garin Katsina domin faɗaɗa birnin.
Gwamnatin jihar za ta sayi kayan aiki domin gina da gyara tare da tona madatsun ruwa na noman rani a mazaɓu 361 da ke jihar
