SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU
Samar da ingantaccan illimi dan samar da alumma ta gari shine babban burin da gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Malam Umar Namadi Ɗanmodi ta sa gaba kamar yadda shugaban hukumar kula da ingancin illimi Dr. Yau Ahmad Sara ya bayyana.
Dr. Sara yace babban abun da yasa a gabansa a yanzu shine ya ga yara suna samun ilimi mai inganci tun daga tushe, ba yawan cin jarabawaba. Shugaban yayi wannan kira ne yayin da wata cibiyar wayar da kan al’umma da kyakykyawan shugabanci take karrama shi a ofishin sa dake Dutse babban birin jihar.
Ya kuma bayyana irin nasarorin da ya samu daga zuwan sa kawo yanzu wanda ya haɗa da samar da ita kanta ma’aikatar a matsayin hukumar mai zaman kanta wanda a da tana ƙarƙashin kulawar ma’aikatar illimi, sanar da sabbin hanyoyin da za su taimaka wajen samar da ingantaccan illimi, shigar da hukumar cikin kasafin kuɗin jihar dan aiwatar da ayyukan ta kai tsaye.
Da yake miƙa lambar karramawar shugaban cibiyar Kwamared Auwalu Yalwa yace sun zaɓi shugaban hukumar kula da ingancin illimi ne sabo da yadda yake aiki tuƙuru wajen ganin yara a jihar suna samun illimi mai inganci.
Yalwa ya ƙara da cewa Dr. Sara ya kawo cigaba sosai bama iya a ɓangaren ilimi ba, har ma da wasu sassan domin cigaban jihar dama al’ummarta. Inda yayi fatan cewa wannan karramawar da a ke wa shugaban za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ƙara ƙaimi dan gudanarwa alumma ayyukan da za su bunƙasa rayuwarsu musammam harkar samar da ingantaccan ilimi.
Da ya ke nuna farin cikinsu kan karramawar da aka yiwa shugaban nasu, ɗaya daga cikin daraktocin ma’aikatar Malam Abdukmudallib Babale wanda shine darakta mai kula da tabbatarwa da bin doka da ƙa’ida, ya bayyana cewa zuwan Dr. Yau Sara an sami canje canje masu yawan gaske a ma’aikatar wanda yin hakan ya kawo cigaba sosai da samar da nagartaccan ilimi ga yaran jihar.
Ya ƙara da cewa zuwan nasa a matsayin shugaban hukumar yasa ma’aikatar tana samun aikace aikace da dama, samun damar gabatar da ayyukan ta kai tsaye daga ofishin gwamnan jihar, shigar da ita cikin kasafin kuɗi dama nasarori masu tarin yawa.
