Muhallin darbejiya a gyaran jiki

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A wannan mako za mu ɗauko ɗaya daga cikin itacen da muke ɗauka da muhimmanci amma kuma muke masa kallon marar amfani.

Sau da yawa idan ka tambaye mutane amfanin itacen darbejiya, sukan ce icen na da amfani ne a lokacin zafi, wato don samar da inuwa da kuma iska. wasu kuma na ganin cewa, wani icce ne da mutanen baya suka yi amfani da shi a matsayin magani, wanda a yanzu ilimi ya zo aka fahimtar da illa ne ga lafiya.

Bari mu soma da maganganun magabata, a can baya, magabata na amfani da ganye da sassaƙen iccen darbejiya a curuta da dama, kamar matsalar da ta shafi ciki, akan daka ganyen a sa ruwa, sai a tace ana sha don kawar da cutar. Da wasu curuta da dama wanda a inda aka fito suna tasiri sosai.

Da zuwan kimiya sai aka gano yin hakan na da illa ga jikin ɗan adam, saidai ba a yadda muka fahimci abin ba. Su masana ba su taɓa kushe ganyen ba, asalima masana magunguna sun tabbatar da amfani da shi don yin wasu magungunan da mu muke zuwa ɗakin shan magani mu siyo. A cewarsu, shan shi a yadda yake zai iya zama illa saboda yana ɗauke da sinadarai masu yawa a tare, kunga a nan maganar magabata ta tabbata na cewa magani ne kan curuta da dama, saidai inda matsalar take, a lokacin da ka sha, abinda ka ke buƙata na maganin cutar da ka ke da ita zai maka magani, wanda ba ka buƙatar fa? Zai iya zama illa gare ka duk da cewa magani ne ga wasu.

Da wannan ne suke amfani da saninsu don fitar da abinda ka ke buƙata ga wata cuta, su nisantaka da abinda ka iya zama illa ga jikinka. Kamar dai yadda kwayoyin magani suke, za a faɗa ma adadin da ya kamata ka sha, da yawan da in ka sha zai iya yi ma illa.

Bari mu koma ga darasin namu, wato tasirin iccen ga fata, wato ta fuksar gyara. Shin iccen darbejiya na da wata rawa da yake takawa ga gyara ko lafiyar fata?

Za mu ci gaba

By ukarofi