Daga ABDULLAHI MUHAMMAD
Majalisar zartaswa a zaman ta karo na 13 ƙarƙashin shugabancin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da inganta gidan talabijin na jihar zuwa tsari na dijital.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Dr Bala Salisu Zango ya sanar da haka bayan kammala taron majalisar zartaswa karo na 13.
Kwamishinan ya bayyana cewa yanzu haka gwamnatin na shirin shigar da na’urar watsa shirye-shirye mai ƙarfin 5KW da wata mai karfin 2.2KW a matsayin madadi.
Haka kuma Dr Bala ya ƙara da cewa za a sanya na’urar amfani da hasken rana (solar) domin tabbatar da ɗorewar wutar lantarki.
Kwamishinan ya ce sabuwar na’urar za ta maye gurbin wacce aka girka tun sama da shekaru 30 da suka wuce, wacce yanzu ta riga ta zama tsohuwa.
Da wannan sabon ci gaba da aka samu a cewar sa gidan talabijin na KTTV zai riƙa watsa shirye-shiryensa kai tsaye ta tauraron dan adam, kuma za a riƙa ganinsa ta decoders da kuma talabijin na gida.
Kwamishinan Ilimi Fasaha da Sana’o’i, Dr. Muhammadu Isa, musanta tafe raɗi da ake ta yaɗawa cewa gwamnatin Jihar Katsina ta rufe cibiyar Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma.
“Gwamnatin jihar da dai rufe wasu cibiyoyi masu zaman kansu da ba su da izini, waɗanda ke gudanar da shirye-shiryen ilimi ba tare da amincewa daga hukumar NCCE ko NUC ba,”inji kwamishinan.
Ya ƙara da cewa da yawa daga cikin waɗannan cibiyoyin suna amfani da gine-ginen makarantun gwamnati, wanda hakan bai dace ba.
Daga nan sai buƙaci Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ta samar kayayyakin aiki na kanta idan tana son ci gaba da gudanar da cibiyoyi, maimakon dogaro da makarantun gwamnati.
Shima a wajen taron manema labarai Mashawarci na musamman kan Ilimin firamare da sakandare, Hon. Nura Saleh Katsayal, ya sanar da amincewa da bayar da kwangilar samar da litattafan karatu na musamman ga makarantun EECD, firamare, da ƙananan sakandare a ƙananan hukumomi 34 na jihar.
A cewar sa wannan shiri zai taimaka wajen inganta karatu da rubutu da kuma inganta ƙwazon ɗalibai a makaranta.
Haka ma Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya sanar da cewa taron majalisar zartaswa ta kuma amince da kammala filin tashar motoci na hukumar sufuri ta jihar Katsina (KSTA) da ke Dandagoro da ke kan hanyar zuwa Kano.
Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu, Alhaji Yusuf Haruna Jirdede,duk a wajen taron manema labarai ya sanar da amincewa da bayar da otal ɗin Malumfashi ga masu zuba jari masu zaman kansu.
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan nasarar da gwamnati ta samu a watan da ya gabata, inda ta bayar da otal-otal ɗin Katsina da Daura ga masu zaman kansu.
