Gwamna Abba ya karɓi rahoton aikin hajji na 2025

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Da yake jawabi jim kaɗan bayan da ya karbi rahoton, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati za ta nazarci rahoton tare da ɗaukar matakan da suka dace a duk inda ake da buƙatar gyara domin cigaba da samun nasara aikin hajji na gaba.

Ya bayyana jin daɗin sa bisa yadda Jihar Kano ta samu lambobin yabo a matsayin jihar da tayi fice wajen kula da walwala da jin daɗin alhazanta fuskar masauki da ciyarwa da kuma tsarin zirga-zirgar mahajjatanta.

Ya godewa hukumar jin daɗin alhazai ta jiha da wakilan kwamitocin aikin Hajjin da aka tura ƙasa mai tsarki bisa jajircewar da suka yi wajen tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.

Da yake gabatar da rahoton shugaban kwamitin kula da alhazai mai Martaba Sarkin. Ƙaraye Alhaji Muhammad Muhammad Mahraz ya ce rahoton mai ɗauke da ɓangarori guda biyu ya ƙunshi dukkanin nasarori da kuma ƙalubalen da aka fuskanta a yayin gudanar da aikin Hajjin domin a ɗauki matakan gyara a aikin hajji na gaba.

Kazalika, ya ce rahoton ya ƙunshi dukkanin bayanan yadda aikin Hajjin ya gudana wanda ya haɗa da bayanin jigilar Alhazai tun daga gida Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki da rahoton lafiya da masaukan Alhazai da abincinsu da kuma bayanin kwamitin da aka haɗa domin taimakawa Alhazai a yayin aikin hajji.

Ya ce rahoton ya gabatar da koke ga Hukumar aikin hajji ta ƙasa inda ya buƙaci ta gabatar da roƙo ga gwamnatin Saudi Arabia ta rinƙa sassauta tsarinta na rufe hanyoyi a yayin aikin hajji domin saukakawa mahajjata wahalhalun sufuri da suke fuskanta.

A jawabinsa, shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jiha Alhaji Lamin Rabiu Dan Bappa ya bayyana cewa hukumar Alhazai ta ƙasa ta bawa jihar Kano kujeru 5,684 yayin da ta ƙayyade Naira miliyan takwas da dubu dari biyar a matsayin kuɗin ajiya.

By ukarofi