Gwamnatin Legas ta yi watsi da rahoton kashe masu zanga-zangar EndSARS tara a Lekki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin jihar Legas ta fitar da farar takardarta kan rahoton da kwamitin bincike kan zanga-zangar EndSARS ya gabatar ma ta wanda ya binciki lamarin da ya faru a ƙofar Lekki a ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, a safiyar ranar Talata yayin ganawa da manema labarai, ya yi alƙawarin cewa za a fitar da farar takarda a ranar Talata.

Sai dai gwamnan ya yi watsi da rahoton kwamitin na cewa mutum tara kawai aka kashe a ƙofar karɓar haraji lokacin da sojoji da ‘yan sanda suka harbe masu zanga-zangar lumana.

Sanwo-Olu ya bayyana a ƙarshen taron cewa, an harbe mutane tara ne a matsayin zato da kuma hasashe.

Yayin wani taron manema labarai da aka yi a ranar Talata a gidan gwamnati, Sanwo-Olu ya ce, “cikin babban nauyi ne na yi muku jawabi a yau game da martanin da ya biyo bayan fitar da rahoton kwamitin EndSARS na Legas da aka gabatar min game da shi makonni biyu da suka wuce kuma yanzu ya fara fitowa a cikin maganganun jama’a tun lokacin.

A ranar Litinin biyu da ta gabata, kwamitin ya miƙa rahoton ga gwamnatin jihar Legas, inda ya gano ƙarara cewa sojojin Nijeriya da ‘yan sanda sun harba harsashi kai tsaye kan masu zanga-zangar lumana a Lekki a bara.

An ƙaddamar da kwamitin ne a ranar 19 ga Oktoba, 2020, domin duba koke-koke na ‘yan ƙasa kan take haƙƙin ɗan Adam da ‘yan sanda ke yi.

Bayan abin da ya faru a Ƙofar Karɓar Haraji na Lekki a ranar 20 ga Oktoba, 2020, an faɗaɗa Sharuɗɗan Tuntuɓar Kwamitin don ɗaukar wannan lamarin da muhimmanci.

Kwamitin ya zauna sama da shekara guda kuma ya ɗauki shaidar masu shigar da ƙara, shaidu, masana da lauyoyi.

Gabatar da kwamitin da aka yi na cewa lallai an yi kisan kiyashi tun daga lokacin ya ja hankalin ‘yan Nijeriya da ƙasashen duniya da suka yi kira da a hukunta jami’an da suka aikata wannan ɗanyen aiki.