Jami’an tsaro sun hana ma’aikatan da ba a yi musu allurar rigakafi ba shiga sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A halin yanzu an hana ma’aikatan gwamnati da sauran jama’ar da ba su da shaidar allurar rigakafin Korona na PCR daga shiga rukunin ginin gwamnati a Abuja.

Sai dai ƙungiyar manyan ma’aikatan Nijeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin dokar hana ma’aikatan da ba su yi wa allurar rigakafi ba zuwa watan Maris na shekara mai zuwa, daga wa’adin yau na yin allurar dole ga ma’aikatan, matakin da Boss Mustapha ya jagoranta a fadar shugaban ƙasa wanda kwamitin gudanarwa ya bayyana a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

Nijeriya a ranar Laraba kuma ta ba da rahoton ɓullar wata cutar har wuri uku na Omicron na cutar Korona.