Zaɓen Anambra: Soludo ya sake samun nasara a kotu

Daga BASHIR ISAH

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya tsallake siraɗin hana rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan Anambra ya zuwa watan Maris mai zuwa.

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ce ta yanke wannan hukunci a Larabar da ta gabata, inda ta ƙi bayyana zaɓen da Soludun ya lashe a matsayin mara inganci.

Alƙalin kotun, Justice Taiwo Taiwo ya yi fatali da ƙarar da aka shigar a gabansa wanda aka nemi ya soke nasarar da Soludo ya samu a zaɓen da ya gabata bisa zargin miƙa wa hukumar zaɓe INEC bayanan ƙarya.

Adindu Valentine da Egwudike Chukwuebuka su ne suka shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/711/2021, inda suka yi zargin cewa Soludo ya bada bayanan bogi wajen cika takardar ‘Form EC9’ da ya miƙa wa INEC.

Sun yi iƙirarin cewa bayanan da Soludo ya miƙa sun nuna yana takarar kujerar mazaɓar Aguata 2 ne alhali kujerar gwamna yake nema.

Haka nan, sun shaida wa kotu cewa, shi ma zaɓaɓnen mataimakin gwamna ga Soludu, Onyeka Ibezim, ya miƙa wa INEC bayanan ƙarya inda ya ce yana takarar mazaɓar Awka 2 ne alhali ba haka lamarin yake ba.

Sai dai Alƙali Taiwo ya yi watsi da duka zarge-zargen saboda rashin hujjoji. Daga nan, kotun ta yanke hukuncin a biya miliyan N2 ga Soludo da Ibezim da kuma jam’iyyar APGA.

Kotu ta ce masu ƙarar sun gaza wajen gamsar da ita da ƙwararan hujjoji kan ƙarar da suka shigar, tare da cewa sun shigar da ƙarar ne da mummunar manufa wanda hakan kuwa kyakkyawan misali ne da ke nuna rashin son ci gaban dimukuraɗɗiyar ƙasa.