Gwamnatin Shugaba Tinubu za ta gina sabon babban layin wutar lantarki a Nijeriya

Ministan wutar lantarki Adelabu ne ya shaida wa manema labarai bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadar mulki da ke Abuja, ministan ya ƙara da cewa sabon tsari zai ba da damar rarraba wutar zuwa ga gidajen jama’a idan layin da ake da shi a yanzu ya samu matsala.

Adelabu ya ce za a kuma samar da wasu ƙarin layikan wuta a yankuna daban-daban domin rarraba tsarin wutar lantarki. “Duniya ta wuce tsarin layin wuta guda. Yanzu dole ne mu samu na yankuna daban-daban.” inji ministan.

Wannan tsari, a cewarsa, zai bai wa kowanne yanki kariya daga matsalar da wani yanki zai iya samu, domin rage yawan faduwar layin wuta gaba ɗaya.

Ministan ya bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin layin wutar sun kai shekara 50 da kafuwa, musamman a yankin Arewa inda igiyoyi suka fara yin rauni, sanduna na rushewa, kuma tashoshin wutar ba su iya tallafa wa rarraba wuta yadda ya kamata.