Kocin Sporting Lisbon, Ruben Amorim, ya amince da zama sabon kocin Manchester United bayan tsige Erik ten Hag a ranar Litinin, a cewar TalkSport.
Manchester United sun fara tattaunawa da ɗan shekara 39 ɗin game da wannan muƙamin, inda ƙungiyar ta shirya biyan kuɗin sakin kwantiraginsa na €10m.
Amorim yana da sha’awar karɓar aikin, kuma Manchester United za ta yi ƙoƙarin tattaunawa da Sporting Lisbon kan sauyawar kocin zuwa Ingila.
Bayan korar ten Hag, sunan Amorim ya kasance daga cikin waɗanda aka tattauna da su don maye gurbinsa.
Sauran waɗanda aka yi la’akari da su sun hada da tsohon kocin Barcelona Xavi Hernandez, kocin Brentford Thomas Frank, da tsohon kocin Borussia Dortmund Edin Terzic.