Daga USMAN KAROFI
A ranar Litinin, hukumar rarraba wutar lantarki ta Ƙasa (TCN) ta bayyana cewa matsalar tsaro ta kawo cikas ga gyaran layin wutar da aka lalata, amma ta tabbatar da cewa tana aiki tuƙuru don dawo da rarraba wutar lantarki yadda ya kamata. Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci TCN da ta gaggauta gyaran tare da bada umarnin ga mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, don samar da kariya ga injiniyoyin da ke gudanar da aikin.
Shugaban TCN, ya bayyana cewa kamfanin ya tura injiniyoyinsa don kammala gyaran, tare da niyyar rarraba kusan megawatt 500 zuwa 600 na wutar lantarki ga yankin Arewa kafin ranar Lahadi. Ya ce dawo da ɗaya daga cikin layukan zai baiwa TCN damar wucewa da megawatt 400 ta wannan hanyar, kuma suna ƙara himma wajen gyaran layi na biyu a tsakanin Ugwuaji da Apir zuwa ranar Lahadi, 3 ga Nuwamba, 2024.
Ya ƙara da cewa, “Dawowar wannan layin zai bai wa TCN damar isar da isasshen adadin wutar lantarki daga Apir zuwa Jos, Kaduna da Kano. Idan layin Shiroro-Kaduna ya samu matsala, layin Ugwuaji-Apir ke zama hanyar da aka dogara don isar da wuta zuwa Arewa.”
Duk da haka, wannan layi shima an lalata wasu ɓangarensa, inda aka lalata kusan guda biyar. Injiniyoyin kamfanin na ƙoƙarin gyara wannan layi, amma suna buƙatar rakiyar sojoji saboda tsaro. “Injiniyoyinmu suna ficewa daga wurin misalin karfe 6 na yamma don tsaron lafiyarsu, sannan suna komawa wurin da aiki da safe.”
A halin yanzu, layi na ɗaya wanda zai iya daukar megawatt 400 yana gab da kammalawa tsakanin yau da gobe, yayin da ake sa ran gama layi na biyu zuwa ranar Lahadi. Wannan zai bai wa TCN damar isar da megawatt 500 zuwa 600 ga yankin Arewa bayan kammala gyaran.