Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin samar da ci-gaban tattali mai ɗorewa a Filato, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da zaman lafiya da ci-gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa a Jihar Filato da ma Nijeriya baki ɗaya.

A lokacin da ya ke magana yayin ziyarar ta’aziyyar rasuwar Sheikh Sa’id Alhassan Jingir a gidan Shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar Izala (JIBWIS) ɓangaren Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, Shettima ya bayyana ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ci-gaba.

Ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya isar da gaisuwar ta’aziyyarsa gami da tabbatar wa mutanen Filato cewa gwamnatinsa ta fifita samun zaman lafiya da haɓakar tattalin arziƙi a jihar, wadda tana da muhimmiyar rawa da take takawa wajen cimma hakan.

Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa ƙoƙarinta na samar da zaman lafiya acikin al’umma, ya na mai cewa Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da tallafa wa shirye-shiryensu ga ɗorewar hakan.

A yayin addu’a ga rasuwar babban malamin, wanda ya kasance mataimakin shugaban malamai na ƙungiyar, shettima ya yi masa fatan samun rahamar Allah da kuma samuwar zaman lafiyar al’ummar da ci-gaba a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

A nasa jawabin, Sheik Sani Yahaya Jingir, ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Tinubu da Mataimakin nasa bisa jajenta masu da karramawa da suka samu daga gare su, ya na mai jinjina masu ga kyawawan ayyukan da suke yi wa Nijeriya da al’ummarta.

Ya bada misali da aikin titin Jos zuwa Saminaka zuwa Kaduna, wanda gwamnati ta ware wa Naira biliyan 33 a lokacin da suka buƙaci ta waiwayi babbar hanyar.

Sheikh Jingir, ya kuma ce yanzu an samu zaman lafiya a jihar a tsakanin Musulmi da Kiristoci da ma waɗanda ba su ba, sakamakon sun fahimci sai da zaman lafiya ake samun nasara.

By Babaji