
Daga BELLO A BABAJI
Rundunar ƴan sandan Jihar Gombe ta tabbatar mutuwar wata ƴar shekara 16 mai suna Maryam Samuel, wadda ta kashe kanta a garin Kaltungo dake Ƙaramar Hukumar Kaltungo a jihar.
Kakakinta, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya ce yarinyar ta aikata hakan ne ta hanyar rataye kan nata a wata bishiya.
Ya ce, lamarin ya auku ne a ranar 14 ga watan Maris, sa’o’i 24 bayan fitarta daga gida domin ɗebo itace a yankin gundumar Kalarin a ƙaramar hukumar, inda aka gano gawar yarinyar a rataye a wata bishiya dake kan dutsen Kalarin.
DSP Abdullahi ya kuma ce, suna cigaba da gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar yarinyar, inda da zarar sun kammala, za su sanar da al’umma.
Wani daga cikin ƴan ahalinta da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce wani saurayin yarinyar ne ya yi mata ciki a yayin da ta ke kai masa ziyara, lamarin da ya haifar da tsama tsakanin sa da iyayenta.