
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankula da ƙaurace wa fusata juna tare da yin biyayya ga umarnin doka.
A wani taron manema labarai na haɗaka tsakanin Ma’aikatun Shari’a da na Labarai na jihar ne aka bayyana hakan a yayin warware matsalolin hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙara akan rikicin Masarautar Kano.
Manyan jami’an gwamnati a taron sun ce, akwai buƙatar a bayyana wa al’umma haƙiƙanin matsayar kotu domin kauce wa ruɗar da su da labaran da ke tada hankulansu.
A ranar 10 ga Junairu ne Kotun Ɗaukaka ƙara ta yi hukuncin dawo da dokar masarautar Kano ta 2019, inda ta jingine hukuncin Babbar Kotun Tarayya, wanda ya rushe hukuncin da Gwamnatin jihar ta yi a dokar masarautar ta 2024.
Kasancewar bai gamsu da hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙarar ba, Alhaji Aminu Babba Ɗan-Agundi ya shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, inda ya nemi kotun da ta haramta wa gwamnatin Kano, Kakakin Majalisar dokokin jihar, Sufeton ƴan sanda, jami’an Civil Defense da sauran jami’an tsaro cigaba da tabbatar da hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙara, yayin da aka ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙolin.
A yayin haka ne aka samu wasu rahotonni da ke bayyana batutuwan da ba haka suke ba game da shari’ar, inda idan suka yi kira a gare su da su ƙaurace wa tsoma baki a harkokin shari’a.
Don cire wa al’umma kokwanto, jami’an sun ce Kotun Ɗaukaka ba ta janye hukuncinta na ranar 10 ga wata ba, har sai Kotun Ƙoli ta yi hukunci na ƙarshe game da dambarwar masarautar.
Saboda haka gwamnatin jihar ta ke kira ga al’umma da su zama masu kiyaye doka da yin watsi da dukkan wani batu da zai haddasa fitina acikinsu.