
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni, 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin Ranar Dimukraɗiyya ta ƙasa.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya ce ranar 12 ga Yuni tana da muhimmanci a tarihin Nijeriya, domin tana tuna wa al’umma sadaukarwa, jajircewa da gwagwarmayar da ‘yan ƙasar suka yi wajen tabbatar da mulkin dimukraɗiyya.
Gwamnatin ta kuma jaddada aniyarta ta cigaba da kare dimukraɗiyya, tabbatar da bin doka, gaskiya, riƙon amana da shugabanci mai haɗa kan kowa.
A shekarar 2018 ne marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya ayyana 12 ga Yuni a matsayin Ranar Dimukuraɗiyya ta Nijeriya inda ta maye gurbin ranar 29 ga Mayu da aka saba amfani da ita a baya.
