
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ware ranakun 25 da 26 ga watan Disamba da kuma 1 ga watan Janairu, 2025 a matsayin lokacin hutun Kirsimeti da ranar ‘Boxing’ da sabuwar shekara.
Babbar Sakatariyar Harkokin Cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin inda ta ce Ministan Ma’aikatar, Dakta Olubunmi Tinubu-Ojo ya bayyana hakan a madadin gwamnatin.
Ta ce Ministan ya aika da saƙon gaisuwa ga ɗaukacin al’ummar Nijeriya, ya na mai kira a gare su da su yi amfani da damar lokacin wajen yaɗa soyayya, haɗin-kai da zaman lafiya a tsakanin iyalai da garuruwa da kuma yi wa kai da ma ƙasa baki ɗaya addu’o’in samun nasara.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin an samu tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa acikin al’umma.
