Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin ƙarin harajin kiran wayar sadarwa da ofishin kasafin kuɗi na Nijeriya ke ƙoƙarin yi.

Gwamnatin ta dakatar da qarin kaso biyar cikin dari ne da ake shirin yi a baya.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Ali Pantami ne ya sanar da dakatarwar a ranar Litinin yayin taron ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa na haraji kan hanyoyin sadarwa don bunqasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja.

Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa.

Gwamnatin Tarayya ta hannun ofishin kasafin kuɗi na tarayya a baya ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da shirin fitar da kuɗaɗen da ta ke buqata a kan harkokin sadarwa da abubuwan sha a shekarar 2023.

Sai dai Pantami ya ci gaba da cewa ba ya goyon bayan aiwatar da wannan harajin da zai ƙara tsadar harkokin sadarwa ga ‘yan Nijeriya.