Rashin kulawa da jama’a ba dimukuraɗiyya ba ce

Daga BELLO WANG

Mutanen duniya na kallon ƙasar Amurka a matsayin wata babbar ƙasa, wadda ke kan gaba a fannin tattalin arziki, da na ingancin aikin likitanci.

Sai dai ƙasar ta fi shan kaye a fannin tinakar cutar COVID-19 a duniya, ganin yadda mutanen ƙasar miliyan 94.6 suka kamu da cutar, kana wasu miliyan 1.04 daga cikinsu suka mutu sakamakon cutar, inda suka kasance kimanin kashi 1 bisa kashi 6 na adadin duniya baki daya.

Sai dai ƙasar ta sake gyaran manufarta a fannin tinkarar annobar COVID-19 a kwanan baya, inda ta fara dakatar da samar da na’urorin gwajin kwayoyin cuta kyauta daga ranar 2 ga watan Satumban da muke ciki, kana gwamnatin ƙasar za ta daina biyan kuɗin jinyar mutanen da suka kamu da cutar, da na yi wa mutanen ƙasar allurar rigakafi, maimakon haka za a ɗora nauyin kan kamfanonin ishora da jama’ar ƙasar.

Duk da cewa ƙasar na ci gaba da fama da yanayi mai tsanani ta fuskar tinkarar cutar COVID-19. An ce a makon da ya gabata, an samu ƙarin mutane fiye da 85274 dake kamuwa da cutar COVID-19 da kimanin wasu 500 da suka mutu sakamakon cutar a ƙasar a kowace rana.

To, ina dalilin da ya sa ƙasar Amurka ke ci gaba da sauƙaƙa matakan tinkarar annoba, yayin da yanayin cutar ke kara tsananta a ƙasar?

Da farko, gwamnatin ƙasar Amurka na fama da matsalar ƙarancin kuɗi.

Bayan ɓarkewar annobar COVID-19, gwamnatin ƙasar Amurka ta sha cin bashi da yawa, don ɗaukar matakan tinkarar annoba, da sa kaimi ga bunƙasuwar tattalin arziki. Sai dai matakin ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki, da ba jama’a wahalar zaman rayuwa.

Zuwa yanzu, gwamnatin Joe Biden na neman rage kuɗin da hukumomin ƙasar ke kashewa, da takaita hauhawar farashin kaya, lamarin da ya sa ake fama da ƙarancin kuɗi a ayyuka daban daban, ciki har da aikin tinkarar annoba.

Na biyu, shi ne, gogayar da jam’iyyun siysan ƙasar Amurka suke yi ta hana zuba jari ga aikin kandagarkin yaduwar annoba.

Bayan gwamnatin ƙasar ta ce ana fama da matsalar ƙarancin kuɗi na tinkarar annoba, nan take su ‘yan majalissun da suka kasance ‘ya’yan jam’iyyar Republican ta ƙasar suka fara zargin White House da yin ƙarya.

Daga baya aka hana zuba ƙarin jari ga aikin tinkarar annoba.

Sa’an nan dalili na uku wanda ya fi muhimmanci shi ne, a ganin wasu ‘yan siyasan ƙasar Amurka, aikin kare lafiyar jama’ar ƙasar ba shi da muhimmanci, idan an kwatanta shi da aikin ƙasar na neman yin babakere a duniya, da yada tunanin Dimokuraɗiyya irin na ƙasar.

A watan Maris na bana, an zartas da kasafin kuɗi da darajarsa ta kai dalar Amurka triliyan 1.5 a majalissun dokokin ƙasar Amurka.

Sai dai a cikin kundin kasafin kuɗin, an soke shiri na dala biliyan 15.6 na tallafawa ƙoƙarin tinkarar cutar COVID-19 sakamakon sabanin ra’ayin da ake samu tsakanin jam’iyyun siyasa na ƙasar, kana a maimakonsa an zartas da kuɗin tallafi na dala biliyan 13.6 da za a ba ƙasar Ukraine.

Yanzu haka majalissun dokokin ƙasar Amurka sun riga sun amince da tallafi na dala biliyan 50 da ake neman baiwa ƙasar ta Ukraine.

Wannan ya nuna cewa, idan tana so, ƙasar Amurka za ta iya samun kuɗin da take bukata wajen tinkarar annoba.

Sai dai a idanun ‘yan siyasan ƙasar, aikin yayyata tunanin Dimokuraɗiyya irin na ƙasar Amurka ya fi muhimmanci.

Sanin kowa ne, kafin a ce wata kasa mai tsari na dimokuraɗiyya ne, ya kamata a duba manufofinta na taimakawa kare moriyar jama’a.

Yadda ƙasar Amurka ta zuba kuɗi ga Ukraine, ya taimaki ‘yan siyasan ƙasar cimma burinsu na tabbatar da yin babakere a duniya, da fitar da tunanin Dimokuraɗiyya irin na ƙasar Amurka.

Haka kuma ya sa kamfanonin ƙera makamai na ƙasar cin riba sosai.

Sa’an nan bayan da gwamnatin ƙasar Amurka ta mika aikin kare jama’a daga annoba ga kasuwa, su kamfanonin samar da magunguna da masu ba da hidimar jinya za su samu maƙudan kuɗi.

Sai dai an kasa kula da wasu. Saboda har yanzu a ƙasar Amurka akwai kimanin mutane miliyan 30 da ba su iya sayen hidimar inshorar lafiya ba.

Daina samar da hidimomi kyauta na nufin za a kyale lafiya da tsaron wadannan mutane marasa karfi.

Ga ta nan dai, wata ƙasar da ta kasa kulawa da jama’arta, har ma tana so a dinga kallonta a matsayin mai jagorantar aikin raya dimokuraɗiyya.

Yadda gwamnatin ƙasar Amurka ta kasa sauke nauyin dake bisa wuyanta na tinkarar annobar COVID-19 ya sa jama’ar ƙasar shan wahala sosai.

A sa’i ɗaya kuma, ya sa mutanen duniya fahimtar cewa alƙawarinta na kare dimokuraɗiyya a duniya ba shi da gaskiya, saboda rashin kulawa da jama’a ba dimokuraɗiyya ba ce.