Ƙasar Sin ta yi nasarar gwajin harba tauraron ɗan Adam na Weili mai lamba 1 S3/S4

Daga CMG HAUSA

Yau ne da misalin ƙarfe 10 da mituna 24 na safe, ƙasar Sin ta yi amfani da rokar Kuaizhou-1A a cibiyar harba tauraron ɗan adam ta Jiuquan, inda ta yi nasarar gwajin harba tauraron ɗan-Adam samfurin Weili Space-1 S3/S4 cikin sararin samaniya kamar yadda aka tsara, kuma aikin harba tauraron d’ɗan-Adam din ya samu cikakkiyar nasara.

Wannan shi ne karo na 17 da aka ci nasarar yin amfani da rokar Kuaizhou-1A, wajen aikin harba taurarin ɗan-Adam zuwa sararin samaniya.

Mai fassara: Ibrahim Yaya