Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da mataki na biyu na ɗaukar ma’aikata ƙarƙashin shirin Renewed Hope Employment Initiatiɓe (RHEI) ƙarƙashin Hukumar Kula da Ayyukan Yi (NDE), domin rage rashin aikin yi da kuma koyar da matasa dabarun samun sana’o’i da cigaba.
Shugaban Hukumar NDE, Mista Silas Agara ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shafin rajista ta yanar gizo a birnin Abuja, inda ya ce tsarin zai kasance cikin gaskiya da adalci, kuma an tsara shi ne domin bai wa kowane ɗan ƙasa dama ba tare da nuna bambanci ba. “Mun kammala mataki na farko cikin nasara, kuma mun samar da kayan aiki da cibiyoyi a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya don gudanar da wannan mataki na biyu cikin sauƙi,” inji shi.
Agara ya ce duk wanda ke son shiga shirin zai buƙaci lambar NIN da kuma shedar zama a cikin wata jiha ta Nijeriya, ko da ba asalin can jihar yake ba.
Ya bayyana cewa ’yan Nijeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 45 ne kadai za su iya yin rajista, kuma za su samu horo a fannoni sama da 30 na sana’o’in hannu da fasahar zamani, bisa buƙatun tattalin arzikin kowace jiha.
“Misali, abin da ke da amfani a Abia ba lallai ya dace da Adamawa ba, shi ya sa muka tsara horon bisa ga buƙatun kowacce jiha,” inji Agara.
An buɗe shafin rajista ta yanar gizo kamar haka: www.nderegistrationportal.ng
Za a cigaba da rajista tun daga 28 ga Yuli zuwa 11 ga Agusta, 2025, yayin da za a fara tantance bayanan masu nema daga 12 zuwa 22 ga Agusta.
Ya gargaɗi jama’a da su guji yaudarar masu karɓar kuɗi ko amfani da hanyoyin da ba na hukuma ba.
“Shirin kyauta ne gaba ɗaya, kuma duk wani yunƙuri na damfara, a gaggauta kai rahoton ga ofisoshin NDE na jihohi ko hedikwata,” inji shi.
